Yadda ‘yan Najeriya suka rage amfani da man fetur

0
169

Alkaluma daga hukumomin da ke kula da harkokin fetur na Najeriya sun nuna cewa ‘yan kasar sun rage amfani da fetur tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayyana janye tallafin mai a watan Mayu.

Ranar 29 ga watan Mayu lokacin da shugaban kasar ya sha rantsuwar kama aiki ya bayyana cewa an janye tallafin man fetur da aka dade ana amfani da shi a kasar.

Ya ce tallafin man ba ya amfanar ‘yan kasar don haka zai yi aiki da kudin da za a tara sakamakon janye tallafin don inganta rayuwarsu.

Hakan ya sa farashin fetur ya tashi sannan kusan dukkan kayan da ake saya sun kara kudi sosai.

Baya ga haka, masu amfani da ababen hawa da dama sun ajiye su saboda tsadar da fetur ya yi.

Wani rahoto na kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato hukumar da ke sanya ido kan harkokin fetur ta Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) tana cewa adadin fetur da ‘yan kasar ke amfani da shi kullum ya ragu zuwa lita miliyan 48.43 a watan Yuni.

Hakan ya yi kasa da yadda aka saba amfani da kimanin lita miliyan 66.9 a baya.

Gwamnati ta ce a shekarar da ta gabata kadai ta kashe fiye da dala biliyan 10 a kan tallafin mai.

Shugaba Tinubu ya ce galibin man da ake shigarwa kasar ana yin fasa-kwaurinsa zuwa makwabtan kasashe irin su Kamaru, Benin da Togo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here