Zamu shirya wasan kwallon kafa da ‘yan daban Kano – CP Gumel

0
154

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce za ta buga ƙwallon ƙafa da ƴan daban da suka addabi birnin Kano a wani ɓangaren na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya.

Kwamishinan ƴan sanda Muhammad Useni Gumel ne ya bayyana haka lokacin da yake holin wasu mutane 108 da ake zarginsu da aikata laifuffuka lokacin bikin Sallah Babba.

CP Gumel ya ce, “Zamu fito da sababbin hanyoyin da zamu tabbatar waɗannan ƴan dabar sun gyara halayaensu sun zama mutanen kirki.

“Zamu shirya gasar wasanni tsakaninmu da su. Zamu buga ƙwallon ƙafa da kuma wasannin cikin rufaffen ɗaki.”

Harkar daba dai ta ƙara tsamari a birnin Kano da kewaye tun lokacin zaɓen 2023.

A baya-bayan nan ma ƴan daba sun daddatsa wani ɗan sanda a Kano lokacin da suke faɗa da junansu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here