Amurka za ta bai wa Ukraine bama-baman da aka haramta

0
119

Amurka tabbatar da bayanan da ke cewa za ta bai wa Ukraine bama-bamai masu ‘ya’ya, domin taimaka mata a yakin da take yi da Rasha.

Kasashe sama da dari daya ne a duniya ciki har da kawayen Amurka suka haramta amfani da bama-baman, wadanda ke tarwatsewa su watsa ‘ya’ya bayan an harba su.

Gwamnatin Ukraine ta jima tana matsawa kan a bata bam din, abin da kungiyoyin kare hakkin dan’Adam ke suka da cewa makamin na hallaka jama’a, kamar kadar ‘ya’yan kadanya.

Sannan zai iya kasancewa hadari ga farar hula tsawon shekaru.

Shugaba Biden ya ce wannan sahawara ce mai wuyar gaske da suka yanke, wadda saboda haka ne ma ya sa batun ya dau lokaci kafin a yanzu su zartar da shi bayan nazari tare da la’akari da ce-ce-ku-ce da illolin da za a alakanta da matakin.

Kasashe sama da 100, wadanda suka hada da na kungiyar tsaro ta Nato, suka haramta amfani da wannan irin bam mai ‘ya’ya.

Duk inda aka harba shi yakan watsu a wuri mai fadin gaske, inda wasu ‘ya’yan kan dau lokaci ba su fashe ba, wanda hakan ke zama wata babbar barazana ga fararen hula.

Bugu da kari kuma yana kisan jama’a barkatai, ba tantancewa kamar kadar ‘ya’yan kadanya.

Dan majalisar dokokin Ukraine Oleksiy Goncharenko, ya yi maraba da matakin na Amurka:

”Ukraine na bukatar makamai sosai kuma wannan bam, abu ne da zai raba gardama a fagen daga,” in ji shi.

Ya kara da cewa, ”Kuma a shari’ance Ukraine tana da dukkan wani ‘yanci na amfani da shi saboda mu da Amurka ba wanda ya sa hannu a yarjejeniyar da ta haramta amfani da bam mai ‘ya’ya.”

”Kuma idan ana maganar batun dacewa ne muna da dukkanin wani ‘yanci na amfani da shi saboda rashawa suna amfani da shi sosai,’’ in ji Goncharenko.

Mai bayar da shawara kan harkar tsaro na fadar gwamnatin Amurkar, Jake Sullivan, wanda duk da haka ya ce makamin wata muhimmiyar gada ce a yakin na Rasha da Ukraine, ya yarda cewa lalle akwai matsaloli dangane da bayar da bam din ga Ukraine to amma dole ce ta sa domin al’ummar Ukraine ta tsira daga mamayar ta Rasha.

Ya ce akwai hadarin gaske kusan fiye da na bama-baman idan har manyan motocin yaki na igwa na Rasha suka kara nausawa cikin Ukraine tare da kama karin yankunan kasar.

Suka kuma kara jefa faren hular Ukraine cikin akuba, saboda kasar ba ta da makaman atilare da za ta kare kanta, Sullivan ya ce wannan ba abu ne da Amurka za ta lamunta da shi ba.

Sannan dangane da illar bama-baman da za su watsu ba su fashe ba tsawon shekaru bayan yakin Sullivan ya ce, Ukraine za ta yi aikin kwashe su tare da taimakon Amurka.

Karancin makaman atilaren, wato na harbawa daga nesa shi ne Amurkar ta fake da shi wajen yanke wannan shawara ta bai wa Ukraine bama-baman masu ‘ya’ya.

Baya ga haka, fadar White House din na cewa ita ma Rasha ai ta jima tana amfani da irin bama-baman, wadanda suka ma fi hadari, tun lokacin da ta mamayi Ukraine din.

Burin dai shi ne bai wa Ukraine wannan nau’in bam, da yake haramtacce ga kasashe da dama, da kuma kungiyoyin kare hakkin dan’Adam shi ne taimaka wa kasar a martanin da take mayar wa Rasha na hare-hare.

To amma kuma ba shakka matakin zai kasance wani abu da zai haifar da rashin jin dadi tsakanin kasashen Yamma da masu hankoron tabbatar da ‘yancin bil’Adama, ganin irin yadda farar hula za su kwan a ciki idan aka fara amfani da bama-baman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here