Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa gwajin kimiyyar da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa taliyar Indomie lafiyarta kalau babu wani hadari a tare da ita.
A lokacin da take jawabi ga manema labarai, Adeyeye ta jaddada ingancin lafiyar Indomie da ake samarwa a cikin gida Nijeriya. Ta tabbatar wa masu saye da sayar da kayayyakin abincin cewa, taliyar da aka janye ta “mai dandanon kaza ta musamman (Special Chicken Flabour)” a Taiwan da Malaysia ba ta tsallako cikin Nijeriya ba, don haka ba a sayar da ita ko’ina a kasuwannin Nijeriya.
A cewar shugabar ta NAFDAC, “An gwada jimillar samfura guda 114 na taliyar da abubuwan da suka hada da sinadarai daban-daban na ingancin abinci. Mun samu samfurori 58 daga masana’antu daban-daban, samfurori 24 daga kasuwannin Legas, samfurori 16 daga Abuja, da kuma samfurori 16 daga Kano. An yi amfani da hanyoyi guda biyu don gwada samfurori daban-daban da aka tattara, su ne: dabarar nazari da ake amfani da ita don rarrabewa da gano abubuwan da ke tattare da sinadarai, da kuma dabarar nazarin da ake gano abubuwan sinadarai ta hanyar tantancewa.”
Da take bayani kan jinkirin da aka samu wajen fitar da sakamakon binciken, Adeyeye ta bayyana cewa, hakan ta faru ne saboda wasu kayan aiki da fasahar zamanin da aka yi amfani da su dole sai da aka shigo da su cikin kasar nan daga waje, sannan hukumar ta NAFDAC ta natsu ce ta yi aikin a kimiyance.
Domin nuna gamsuwa da kuma amincewarta da sakamakon gwajin da aka yi, shugabar ta NAFDAC ta cinye taliyar indomie da aka girka aka zuba mata a lokacin taron, inda abokan aikinta suka bukaci su ma ta raba musu ko da taba-ka-lashe.
Manajan Sadarwa da Shirya Bukukuwa na Kamfanin Dufil Prima Foods Plc, Temitope Ashiwaju ya bayyana kudurin kamfanin na kiyaye ka’idojin tabbatar da inganci na kasa da kuma duniya tare da tallafa wa bunkasa tattalin arzikin cikin gida.
Da yake karin haske daga ofishin Dufil Prima Foods da ke Legas, Ashiwaju ya ce, “Ana samar da nau’ikan taliyar Indomie ne a Nijeriya kuma an shafe akalla shekaru talatin ana sarrafa taliyar a kasar. Dupil Prima ya kara fadada ayyukan da yake yi a cikin gida wanda hakan zai bunkasa yawan kayan da yake sarrafawa da daukar ma’aikata domin cimma bukatun kasuwa da zarce ka’idojin da aka gindaya na inganci a gida da waje.