Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 4 da ceto mutum 24 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

0
138

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta na ‘Operation Hadarin Daji’ sun ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ‘yan bindiga hudu a jihar Zamfara ranar Juma’a.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig. Janar Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce dakarun bataliya ta 223, da ke aiki a karkashin sashin 1 na hadin guiwa, Operation Arewa maso Yamma, Hadarin Daji, a safiyar ranar 7 ga watan Yuli, 2023, sun yi artabu da wasu ‘Yan bindiga da suka yi kaurin suna a Kabugu Lamba, kauyen da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Ya ce a yayin aikin ceton da musayar harbe-harbe da aka yi, an kashe ‘yan bindiga hudu, yayin da aka ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su da suka hada da mata tara da maza 14 ciki har da yaro daya.

“Rundunar sojojin da ke karkashin kwamandan Bataliyar sun kai wa ‘yan ta’adar hari tare da hallaka hudu daga cikin su a yayin musayar wutar,” inji shi.

Ya kara da cewa wadanda harin ya rutsa da su da suka hada da kananan yara, mata tara da maza 14, an zakulo su daga maboyar masu garkuwar da sojojin suka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here