Yan sanda sun tarwatsa masu yi wa jama’a kutse a asusun banki

0
142

Shelkwatar rundunar ‘yan sanda ta Zone 2 da ke Onikan a Legas ta fatattaki wata kungiya da ta yi kutse a asusun kwastomomi na banki tare da damfarar su miliyoyin kudade.

Tuni dai an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu wajen zambar, yayin da ‘yansanda suka bayyana su a matsayin mambobin kungiyar.

A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yansandan shiyyar (ZPPRO) wadda ta kunshi jihohin Legas da Ogun, SP Hauwa Idris Adamu, ta fitar, ta ce ’yan kungiyar sun damfari mutum sama da 1000, wadanda suka watsu a fadin kasar nan.

Da take ba da bayanin yadda aka yi nasarar tarwatsa su, Adamu, ta ce, a ranar 8 ga Mayu, 2023, bankin United Bank for Africa (UBA) ya gabatar da koke ga Mataimakin Sufeto Janar na ‘yansanda, Mista Ari Ari Mohammed Ali, cewa akwai wasu kungiyoyin da suka kware kan zamba ta intanet na bankuna daban-daban a Nijeriya musamman United Bank for Africa (UBA), inda suka yi kutse cikin asusun kwastomomi tare da kwashe kudadensu.

“Bisa ga takardar koke, AIG ya tada wata tawagar ‘yansanda daga sashen sa ido na shiyyar, wadanda suka shiga aiki tare da taimakon fasahar zamani, mutum biyu da ake zargi; Yusuf Ademola mai shekaru 40 da Adesina Olawale Abiodun, 50, an gano su ne a maboyarsu da ke Ijebu Ode a Jihar Ogun.

 “Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa, kuma sun ce suna da kungiyoyi da dama a ko ina cikin fadin Nijeriya, wadanda suke amfani da manhajojin kwamfuta wajen yin kutse a cikin asusun abokan hulda da kuma fitar da kudadensu ba tare da an gano su daga bankin da suke so ba.

 “Duk da haka, tsarin da wadannan ‘yan damfara ke amfani da su shi ne samun lambar wayar abokin ciniki ta BBN da kuma sanarwar banki domin a samu saukin cire kudin.

Sakamakon haka, an yi kutse tare da zamba a asusun abokan ciniki sama da 1000 a duk fadin kasar nan. “Binciken da aka yi a kan lamarin ya nuna cewa an fito da ‘yan kungiyar ne daga sassa daban-daban na kasar nan, ana kuma kokarin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a wannan aika-aika.

“A cikin aiki na wucin gadi, ana ci gaba da bincike kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here