Yadda ƙaruwar shigo da shinkafar waje ke neman gurgunta mu – Manoma

0
214
Rice
Rice

Manoman shinkafa a Najeriya sun koka game da fasa-kwaurin shinkafa ‘yar waje da suka ce na karuwa zuwa cikin kasar, abun da suka bayyana cewa hakan na shafar noman shinkafar ta cikin gida.

Kungiyar masu noman shinkafa yar gida a Najeriya sun kuma ce bude kan iyakokin kasar barazana ne ga jarin da suka zuba a aikin sarrafa shinkafa yar gida.

Jami’an kwastam kuma a nasu bangaren na cewa suna iya kokarinsu wajen dakile shiga da shinkafar yar waje.

Shugaban kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya reshen jihar Kano Alhaji Baba Sumaila, ya shaida wa BBC cewa jami’an kwastam na yin iya bakin kokarinsu, sai dai masu shigo da ita ta barauniyar hanya ne ke kawo illa.

”Wadansu mutane ne ke goyon bayan a ci gaba da shigo da shinkafar waje domin su ba su yadda su ci ta gida ba, don haka duk jarin da aka zuba a noman shinkafa idan aka ci gaba da tafiya a haka, asara kawai za a yi” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa su a iya saninsu, shinkafar da ake nomawa a cikin gida ta fi ta waje, duba da yadda ake ingantata, don haka babu maganar cewa ta gidan da ake nomawa ba ta da inganci.

Ya ce ”Shinkafar nan ta waje akwai wadda ta yi shekara goma ma a ajiye, ka shiga kasuwar Singa ko sabon gari ka gani, za ka tarar da shinkafa ta waje da dama duk ta waje aka shigo da ita”

Hukumar Kwastan ta Najeriya a nata bangaren ta ce tana da labarin fasa-ƙwaurin shinkafar amma bai yi munin da zai sa shinkafar waje ta mamaye kasuwannin kasar ba.

Mai magana da yawun hukumar Maiwada Aliyu Abdullahi, ya ce hukumar Kwastam tsaye take domin tabbatar da hana shiga da shinkafar, amma ba abu ne da za a iya hanawa dari bisa dari ba.

”Shinkafar da muka kama ta fi wadda ake shigo da ita, muna da shinkafa ‘yar kasar waje da ta kai sama da buhu dubu dari biyu, su kansu masu neman ‘yan wajen sun ragu’ a cewarsa.

Tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta Najeriyar ce dai ta ɓullo da matakai iri daban-daban don bunƙasa noman shinkafa a cikin gida.

Daga ciki har da bai wa manoma da masu masana’antun sarrafa shinkafa kariya ta hanyar taƙaita shigar da ita daga ƙasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here