Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Mangu, biyo bayan hare-haren da aka kai a yankin.
Gwamna Caleb Mutfwang ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Mista Gyang Bere ya fitar ranar Lahadi a Jos.
Gwamnan a baya, yayin da yake gudanar da ibada a cocin Brethren in Nigeria (EYN), ya bayyana cewa an yi jana’izar mutane 11 da sanyin safiya, biyo bayan harin da aka kai daren Asabar a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar.
Wannan baya ga jerin hare-haren da aka kai a karamar hukumar da kuma a karamar hukumar Riyom inda aka ce an kashe mutane sama da 100, an lalata gonaki da dukiyoyi a kauyukan.
A cewar sanarwar, umarnin da gwamnan ya bayar ya zama wajibi don bin doka da oda a yankin biyo bayan rahoton da kwamitin tsaro na jihar ya bayar kan lamarin.
“Saboda haka, an hana zirga-zirga a cikin Karamar Hukumar har sai jami’an tsaro sun tabbatar da zaman lafiya a yankin.
“Saboda haka an umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana fita baki daya.”
Gwamnan ya tabbatar wa mutanen Filato cewa, gwamnati tana bin dukkan hanyoyin da za a bi domin kawo karshen kai hare-haren da ake ci gaba da yi a wadannan yankuna tare da yin tir da yadda aka yi asarar rayuka da dama tare da lalata dukiyoyi Jama’a a yankin.