APC ta dage taronta na kasa da ta shirya gabatarwa yau Litinin zuwa 18 ga watan Yuli

0
148

Jam’iyyar (APC) ta dage taronta na kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa (NEC) da ta shirya gabatar a ranar Litinin 10 da 11 ga watan Yuli zuwa 18 da 19 ga watan Yuli.

Sakataren jam’iyyar na kasa, Sen. Iyiola Omisore, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya bayar da hakuri kan dage taron.

Ya bayyana cewa dage taron ya zama dole ne saboda sabon nauyin da ya hau kan shugaba Bola Tinubu, a matsayin sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).

“Ana sanar da ‘yan jam’iyyar na kasa da cewa an dage taronmu na ranakun 10 da 11 ga watan Yuli zuwa 18 da 19 ga Yuli 2023,” inji shi.

A Jam’iyyar APC ta kasa doka ne a jam’iyyar, shugaba Tinubu ne zai shugabanci zaman sai kuma mataimakin shugaban kasa, Sen Kashim Shettima da dukkan tsaffin gwamnonin jam’iyyar a matsayin mambobi.

Haka kuma mambobinta sun hada da gwamnonin jam’iyyar da ke ci gaba da rike madafun iko, da mambobin kwamitinta na ayyuka na kasa (NWC) da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here