Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba za su sake yarda da juyin mulki a kasashen Yammacin Afirka ba.
Tinubu ya bayyana haka ne ranar Lahadi jim kadan bayan an zabe shi a matsayin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS mai kasashe mambobi 15.
“Dole ne mu jajirce kan mulkin Dimokuradiyya. Babu gwamnati da ‘yanci da doka idan babu dimokuradiyya. Ba za mu sake yarda da juyin mulki bayan juyin mulki a Yammacin Afirka ba.
Dimokuradiyya na da wahalar gudanarwa amma ita ce tsarin gwamnati mafi kyau,” in ji Shugaban na Ecowas.
Ya kara da cewa: “Babu wani a cikinmu da bai yi yakin neman zabe domin ya zama shugaba ba. Ba mu bai wa sojojinmu kudi da zuba jari a kansu da horar da su don su take ‘yancin jama’a ba…Kada mu zauna a ECOWAS kamar kyanwar-lami.”
Sabon shugaban na Ecowas ya kuma yi gargadi kan yadda yankin na Yammacin Afirka ke fama da rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa ta’addanci da rashin tsaro suna matukar kawo koma-baya ga ci-gaban yankin.
Taron na ECOWAS na 63 shi ne na farko da Shugaba Tinubu ya halarta tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023.