Binani ta maka INEC a kotu kan soke ayyana ta matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa

0
131
Binani, Inec
Binani, Inec

Aisha Dahiru Binani, ‘yar takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Adamawa, ta sake kai karar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Kamar yadda aka ruwaito a baya cewa INEC ta soke shelanta ta a matsayin gwamnan Adamawa a zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga Maris.

Binani, wadda lauyanta, Michael Aondoaka, SAN, ya wakilta, ta gabatar da sabuwar kara a gaban mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/935/2023, ‘yar takarar jam’iyyar APC ta bayyana INEC, jam’iyyar PDP, da dan takararta, Gwamna Ahmadu Fintiri, a matsayin wadanda ta ke kara.

Binani na neman a binciki hukuncin da INEC ta yanke na sauya shelarta na farko a matsayin wadda ta lashe zaben da Kwamishinan Zabe na jihar, Hudu Yunusa-Ari ya yi.

A yayin sauraren karar a ranar Litinin, Aondoaka ya bayar da hujjar cewa kotun sauraren kararrakin zabe ce ke da hurumin tantance makomar wadda yake karewa, inda ya ambaci sashe na 149 na dokar zabe na 2022.

Ya bayyana damuwarsa cewa matakin da INEC ta dauka zai hana Binani tanade-tanade da ke karkashin sashe na 285(6), wanda ya ba da damar kwanaki 180 don warware karar da ta shigar a gaban kotun a ranar 6 ga watan Mayu.

Aondoaka ya sanar da kotun cewa a baya an shigar da irin wannan kara a gaban mai shari’a Inyang Ekwo, wanda ya umarci Binani da ta garzaya kotun don wani lamari da ya shafi zabe.

Don haka, Aondoaka ya nemi a sake duba matakin na INEC kuma ya ba da wani aiki don nuna cewa karar da ake yi yanzu ba ta da tushe.

Ya tabbatar da cewa a shirye suke su biya duk wata tara idan har kotu ta ga cewa karar ba ta da tushe.

Mai shari’a Okorowo ya dage ci gaba da sauraren karar bayan ya saurari hujjojin Aondoaka.

Idan dai ba a manta ba Binani ta janye karar da ta shigar gaban mai shari’a Ekwo a ranar 26 ga watan Afrilu biyo bayan ayyana gwamna Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Lauyan Binani, Mohammed Sheriff, ya gabatar da sanarwar dakatar da shi kuma ya bukaci kotu ta soke karar.

Sai dai mai shari’a Ekwo ya tunatar da Sheriff hukuncin da kotun ta bayar tun farko, inda ya bukaci ya yi magana ko kotu takori shari’ar.

Alkalin ya yanke shawarar yin watsi da batun, bayan da Sheriff ya kasa bi umarnin.

Ida tuna cewa da sanyin safiyar Lahadi, 16 ga Afrilu, 2023, ‘yan Nijeriya suka kadu da ayyana Sanata Aishatu Dahiru Ahmed a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da shugaban hukumar zaben jihar, Ari ya yi.

Leadership

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here