Buhari ya taya Tinubu murnar samun shugabancin ECOWAS

0
157

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya shugaba Bola Tinubu murnar zaɓensa da aka yi a matasyin shugaban bunƙasa arzikn Afirka ta Yamma (ECOWAS)

Kakakin tsohon shugaban, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa manema labarai.

Ya ce “Al’ummar Afirka ta Yamma sun damƙawa sabon shugabanmu gagarumin aiki don haka aikinmu a matsayinmu na ƴan ƙasa mu taimaka masa don ganin bai bada kunya ba.”

Ya ƙara da cewa ‘Ina fatan Ubangjiji zai sa a farfaɗo da ECOWAS a matsayin ƙungiyar tabbatar da dimokraɗiyya, kyakkyawan shugabanci, da yaki da ta’addanci da sauyin muhalli a zamanin mulkinsa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here