Diphtheria: Akalla yara 30 sun mutu a Yobe

0
132

Cutar nan mai sarke numfashi ta Diptheria ta barke a Jihar Yobe, inda ta kashe yara 30 sannan wasu 42 kuma suna can a kwance a Asibitin Kwararru na Potiskum da ke Jihar.

Daga cikin yankunan da cutar ta fi mamaya akwai Tandari, Misau Road, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Igwanda da Texaco, kamar yadda Aminiya ta tabbatar.

Wakilinmu ya gano cewa sama da yara 20 ne suka rasu a gaidajensu, wasu hudu suna kwance a asibiti.

Daya daga cikin mahaifan yara da suka kamu mai suna Abdullahi Muhammad, ya ce yara da dama sun mutu a gida kafin ma a kai ga kai su asibiti.

“Muna kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa wajen ceto rayuwar wadannan yaran namu. Alamun cutar sun hada da zazzabi da tari da kuma raunin jiki.

Shi ma wani dan jarida mazaunin garin na Potiskum, Ibrahim El-Tafsir, ya shaida wa Aminiya cewa, “Kodayake jami’an gwamnati sun ki su fada mana yawan mutanen da suka mutu, amma akwai gidaje biyu da yara hudu da suka mutu, kuma har yanzu muna ci gaba da binne wasu.”

Da wakilinmu ya tuntubi jami’in kula da rigakafi na Karamar Hukumar ta Potiskum, Mallam Buba, ya musanta yawan yaran da ake cewa sun mutu, amma ya amince cewa wadanda aka kwantar a asibiti sun kai 42.

Ya kuma koka kan cewa galibin yaran da suka mutu a gidajensu suka mutu, ba a asibiti ba, inda ya ce iyaye ba sa kai su a kan lokacin da ya kamata.

Shi ma Daraktan Sashen Kula da Lafiya a Matakin Farko na Potiskum, Abdulrahman Musa, ya ce bisa ga rahotannin da suka tattara, suna ci gaba da wayar da mutane a kan illar cutar.

Aminiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here