Man Utd ta kayyade farashin sayar da Maguire

0
139

Manchester United ta kayyade fam miliyan 50 kan ɗan wasanta Harry Maguire, mai shekara 30. (Manchester Evening News)

Donny van de Beek, mai shekara 26, na hanyar barin Manchester United a wannan kakar yayinda Nottingham Forest, Wolves da Crystal Palace ke zawarcinsa. (90 min)

Ɗan wasan Montpellier Elye Wahi, mai shekara 20, da na Juventus asalin Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23, na cikin ‘yan wasan da Chelsea ke zawarci. (Evening Standard)

ddd

Ɗan wasan Torino Perr Schuurs, mai shekara 23, na jan hankalin Liverpool, yayinda Jurgen Klopp ke kokarin inganta kungiyar. (Football Insider)

Leicester City na sha’awar sayen ɗan wasan Ingila Stephy Mavididi, mai shekara 25 daga Montpellier. (Fabrizio Romano)

Newcastle United na iya sayar da ɗan wasanta mai shekara 26 Allan Saint-Maximin – wanda ƙungiyoyin Saudiyya ke zawarci – domin samun kuɗin sayen ɗan wasan Leicester City Harvey Barnes, mai shekara 25. (Telegraph, subscription needed)

Inter Milan na shirin kara kuɗin tayi da ta gabatar kan ɗan wasan Chelsea da Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 30, kan fam miliyan 23 amma Chelsea na son fam miliyan 40. (Times, subscription needed)

Al-Hilal ta faɗawa Manchester City cewa a shirye take ta biya fam miliyan 60 kan ɗan wasan Portugal mai buga tsakiya, Bernardo Silva. (CBS Sports)

Ɗan wasan Ingila, Reece James mai shekara 23, na son zama sabon kyeftin din Chelsea duk da tayin da take samu daga Real Madrid. (Beautiful Game Podcast, via Mirror)

Sheffield na tattaunawa da ɗan wasa Troy Deeney. (Mail)

Ɗan wasan tsakiya a Serbia Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 28 zai koma kungiyar Saudiyya ta Al-Hilal daga Lazio kan fam miliyan 34. (Goal)

Paris St-Germain ke kan gaba a zawarcin ɗan wasan Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani, mai shekara 24. (Independent)

Luton Town na son ɗan wasan Blackburn Rovers’ mai tsaro raga, Thomas Kaminski, ɗan shekara 30. (Lancashire Telegraph)

Wolves na gab da kammala ciniki kan sake sayen ɗan wasan Jamhuriyar Ireland, Matt Doherty, mai shekara 31, bayan barinsa Atletico Madrid. (TeamTalk)

West Ham na fatan cimma yarjejeniya ita ma da ɗan wasan Ingila mai buga tsakiya James Ward-Prowse, mai shekara 28, kan fam miliyan 20, sai dai Southampton tayi masa kuɗi kan fam miliyan 40. (Mail)

Ana samun cigaba a tattaunawar saye mai tsaron raga na Kamaru Andre Onana kan fan miliyan 43 daga Inter Milan zuwa Manchester United, babu mamaki komai ya kamalu a wannan makon. (Mail)

Tottenham Hotspur na da kwarin gwiwar cimma yarjejeniya da ɗan wasan Wolfsburg Micky van de Ven, mai shekara 22, kan fam miliyan 25. (Mirror)

Everton ta tuntubi Manchester United kan ɗan wasansu Tom Heaton, mai shekara 37. (Mirror)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here