An ayyana Aliko Dangote a matsayi na 11 cikin mutum 50 mafi tasiri a duniya – Mujallar Fortune

0
181
Dabgote
Dabgote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya zama attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka karo na 12 a jere, kamar yadda mujallar Forbes ta ruwaito.

Babban kamfanin Dangote na siminti ne ya ci gaba kasancewa kan gaba wajen samar da siminti a Afirka, kuma Dangote shi ne dan Najeriya daya tilo a cikin jerin attajirai 200 na farko a duniya wanda darajarsa tai kai dalar Amurka biliyan 14.2, sama da dala biliyan 12.1 da ya samu a bara.

A halin yanzu Dangote yana matsayi na 124 a cikin manyan attajiran duniya, kuma shi ne dan Najeriya daya tilo a cikin jerin manyan attajiran duniya 200 kuma daya daga cikin ‘yan Afirka biyu da ke jerin attajirai; tare da Johann Rupert na Afirka ta Kudu, wanda ya zo na 157 da darajar dukiyar da ta kai dala biliyan 11.1.

Attajirin wanda ya fi kowa kudi a Afirka na jagorantar kamfanin siminti mafi girma a nahiyar Afrika.

Kamfanin siminti na Dangote na samar da tan miliyan 51.6 a kowace shekara a kasashe goma a Afrika, tare da hadakar masana’antu a kasashe bakwai da kuma wasu masana’antu a Kamaru da Ghana da Saliyo.

Dangote ya mallaki kamfanonin gishiri da sukari da ma wasu daban.

Kazalika, attajirin ya mallaki matatar tace mai, wadda ake kyautata zaton za ta zama mafi girma a duniya, wadda tsohon shugaban kasar Nijeriya, shugaba Buhari ya kaddamar kuma ana sa ran za ta sarrafa gangar mai 650,000 don amfanin cikin gida da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje.

Mujallar Fortune, wata mujalla ce ta kasuwanci ta kasa da kasa da ke Amurka, ta ayyana Dangote a matsayi na 11 cikin mutum 50 mafi tasiri a duniya a tsakanin ‘yan kasuwa maza da mata.

Mujallar da aka fara buga ta a watan Fabrairun 1930, ta ce attajirin na sauya duniya tare da zaburar da wasu a harkokin kasuwanci da gwamnati wajen ciyar da al’ummarsu gaba.

Dangote ya samu matakin ne bayan da mujallar ta ce attajirin yana amfani da dukiyarsa ta hanyar taimakon jama’a da gidauniyarsa ta Aliko Dangote.

Mutum 10 maza da mata da mujallar Fortune ta zayyano a matsayin wadanda suka fi kowa tasiri su ne: Bill da Melinda Gates, Jacinda Ardem, Robert Mueller, Pony Ma, Satya Nadella, Greta Thunberg, Margrethe Vestager, Anna Nimiriano, Jose Andres, da Dough Mcmillon da Lisa Woods.

Shi kuwa Dangote an ayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan kasuwa a fadin duniya wanda ya cancanci a karrama shi ta hanyar basirar kasuwancinsa da kuma ayyukan alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here