An kori dan majalisa yayin zama saboda yin shigar da ba ta dace da zauren ba

0
142

Majalisar Wakilan Najeriya a ranar Laraba ta bukaci wani dan majalisar ya fice daga zauren saboda yin shigar da ba ta dace ba.

Dan majalisar, wanda ba a iya tantance sunansa ba, saboda yana cikin sabbin wadanda da aka rantsar a watan jiya, ya shiga zauren ne da wata rigar T-shet mai launin ja, da kuma wani tsukakken wando.

Bayan shigowarsa, dan majalisar, wanda kuma ya zo a makare, ya nemi wajen zama a zauren majalisar, ana dab da karkare zama.

Sai dai jim kadan bayan ya zauna, sai dan majalisa Billy Osaweru, ya jawo hankalin Kakakin majalisar cewa wanda ya shigo ya yi shigar da ba ta dace ba.

A cewar Billy, shigar dan majalisar ta saba da tsarin saka suttura cikin mutunci na majalisar.

Hakan ne ya sa Kakakin ya bukacin dan majalisar ya fice daga zauren, inda kuma ya yi hakan ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here