Majalisar wakilai ta umarci hukumar NUC ta dakatar da karin kuɗin jami’o’i

0
181

Majalisar Wakilai ta umarci hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa (NUC) ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da jami’o’i suka yi nan take.

Wakilin Mazaɓar Birnin Kano, Ali Sani Madakin Gini (NNPP) ne ya gabatar da wannan ƙudirin a zauren  majalisar.

Madakin Gini ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya sun nunnuka kuɗin makaranta sakamakon hauhawar farashi da ƙarancin kuɗin tafiyarwa da suke samu daga gwamnati.

Ya ce daga cikin jami’o’in da suka yi wannan ƙarin akwai Jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Jami’ar Najeriya dake Nsukka (UNN), Jami’ar Jos, da Jami’ar Noma ta Michael Okpara.

Ɗan Majalisar ya bayyana damuwar cewa an yi ƙarin kuɗin ne lokacin da al’ummar Najeriya ke fama da tsananin talauci, rashin aikin yi, da hauhawar farashi sanadiyyar janye tallafin man fetur.

Ya ce ƙarin kuɗin jami’o’in zai kawo tarnaƙi ga karatun ɗalibai da dama da ba za su iya biya ba.

Bayan gudanar da muhawara, Majalisar ta amince da wannan ƙudiri kuma ta umarci NUC ta dakatar da ƙarin nan take.

Sannan ta umarci kwamitin Ilimi mai zurfi da zarar an kafa shi, ya lalubo hanyar da za a samawa jami’o’i ƙarin kuɗin shiga ba tare da an ɗora wa ɗalibai da iyayensu nauyin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here