Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce dole ne dimokuradiyya ta dore a kasar da ma nahiyar Afirka idan ana so a samu ci-gaba.
Ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci takwarorinsa don kai masa ziyarar taya shi murnar zama sabon shugaban ECOWAS a fadarsa da ke Abuja.
Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Dele Alake ya fitar ranar Alhamis, ta ambato Shugaba Tinubu yana cewa “dole ne dimokuradiyya ta dore.
“Muna bukatar ci-gaba. Dole mu aike da sako mai kyau ga sauran duniya musamman wadanda ke wajen Afirka cewa da gaske muke.”
Shugaban kasar ya ce zaben da aka yi masa na kungiyar raya tattalin kasashen Yammacin Afirka mai mambobi 16 ya zo masa da ba-zata, yana mai cewa abu ne da ke bukatar aiki tukuru.
Shugaba Tinubu ya ce zabensa ya zo “da karin nauyi da dole mu dauka domin ci-gaban Afirka.”
“Bisa samun goyon baya daga gare ku da sauran jama’a na nufin dole na zage dantse,” in ji shi.
Shugaban na Nijeriya ya sha alwashin ganin bai ba wa ‘yan kasar kunya ba wajen gudanar da ayyukansa duk da kalubalen da ake fuskata.
Tun da farko, Sanata Akpabio ya ce zaben da aka yi wa Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS ya nuna yadda ake kallonsa da martaba.