Hukumar tsaro ta Nijeriya DSS ta ce ta gurfanar da shugaban Babban Bankin kasar da aka dakatar Godwin Emefiele a gaban kotu.
DSS ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis da daddare.
Sanarwar, wadda kakakinta Peter Afunanya ya sanya wa hannu, ta ce “bayan umarnin wata babbar kotun Abuja a yau, 13 ga watan Yuli, Department of State Service (DSS) ta tabbatar da cewa an tuhumi Mr Godwin Emefiele a gaban kotu kamar yadda kotu ta bayar da umarni.”
Ta kara da cewa tun shekarar 2022 ta nemi izinin kotu domin ta tsare shi bisa zargin aikata laifuka.
“Ko da yake ya samu umarnin kotun Abuja na hana kama shi, amma hukumar ta kama shi a watan Yunin 2023 bisa sabbin zarge-zargen aikata laifuka, daya daga cikinsu shi ne wannan tuhuma da ake yi masa,” in ji DSS.