EFCC ta cafke wasu ‘yan China 13 a jihar Kwara

0
149

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa (EFCC), a Ilorin sun kama wasu ‘Yan China 13 kan laifun hako ma’adinai ta Haramtacciyar hanya a Ilorin, jihar Kwara.

Laifin ya sabawa sashe na 1(8) (b) na Dokar Laifukan Daban-daban Cap M17, 1983.

Wadanda ake zargin, sun hada da wata mace da maza 12, wadanda aka kama su a ranar Larabar da ta gabata a karamar hukumar Ilorin, babban birnin jihar ta hanyar samun bayanan sirri kan ayyukansu da suka hada da hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da rashin biyan hakkokin gwamnati kamar yadda doka ta tanadar.

Wadanda ake zargin sun hada da Guo Ya Wang da Lizli Hui sai Guo Jian Rong da kuma Lizh Shen Xianian sai Lishow Wu da Guo Pan, sauran sun hada da Lia Meiyu da Guo Kai da kuma Quan sai Lin Pan.

Ragowar mutum biyar din su ne, Ma Jan da Wendy Wei Suqin sai Li Zhinguo Wei da kuma Xie Zhinguo.

Binciken ya kuma nuna wasu daga cikin wadanda ake zargin ba su da takardar ‘iznin aiki’, sai ta ‘iznin ziyara’ daga China zuwa Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here