Jihar Filato: Kashe-kashen rayuka da barnata dukiyar jama’a ya dawo danye

0
125

Wani al’amari da ya zama abin tambaya a wannan makon a wurin galibin ‘yan Nijeriya shi ne me yake faruwa ne a Jihar Filato bisa yadda kashe-kashen rayuka da barnata dukiyar jama’a suka sake dawowa danye, lamarin da ke kara barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar jihar da jihohin da ke makwabtaka da ita.

Masana sun fara nazartar dalilan da suka janyo dawowar kashe-kashen tare da kira da babbar murya ga hukumomin tsaro, da kuma sabuwar gwamnatin jihar da su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen wannan matsalar da ke faruwa ta kashe-kashen rayuka.

Bisa bayanan da kungiyar ci gaban kabilar Mwaghabul (MDA) da Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) suka bayar, sama da mazauna kauyukan Mangu da wasu Fulani 200 ne aka kashe a tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2023 lamarin da ke kara jefa jama’a cikin zaman dar-dar.

Kodayake, a wata tattaunawa mai magana da yawun gwamnan Jihar Filato Gyan Bere, ya ce (zuwa lokacin rubuta wannan rahoton) gwamnati ba ta samu rahoton yawan mutanen da aka kashe a rikicin na baya-bayan nan ba.

 “Abin da na sani shi ne mutanen Mangu na cikin hali mara kyau. Ni na san da cewa ana kashe-kashe a Mangu, ana yi wa mutanen kwanton bauna ana kashe su.”

Mai magana da yawun gwamnan ya ce a yanzu gwamnati ta tura karin dakarun tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin, “Muna rokon al’ummar yankin da su rungumi zaman lafiya, kuma yunkurin da gwamnati ke yi ke nan na ganin an samu zaman lafiya.”

 Rikicin da ke faruwa a Mangu dai ya sanya gwamnatin jihar ta kakaba dokar hana fita karo na biyu cikin wata uku kacal.

A makon jiya Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana zirga-zirga a yankin Mangu sakamakon tashe-tashen hankula.

Idan za a iya tunawa, a cikin watan Mayu gwamnatin Filato ta kakaba dokar hana fita a yankin na Mangu, bayan wasu hare-hare na ‘yan bindiga da aka kaddamar lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama da lalacewar kadarori hade da sanya mutane da dama tserewa su bar muhallai.

 Mazauna Mwaghabul, al’ummar da ta yi fice a harkar noma a karamar hukumar Mangu sun shaida cewa maharan sun kutsa cikin kauyukansu inda suka bude wuta kan mutane tare da cinna wa gine-gine wuta.

 A gefe guda, an zargi jami’an tsaron jihar na musamman da ke aiki a rundunar ‘Operation Rainbow’, cewa sun mamayi rugar Fulani da ke Karamar Hukumar Mangu a Jihar Filato tare da banka wa gidaje da dama wuta.

Fulanin sun ce rundunar ke kai musu hare-hare da kona musu gidaje da bukkoki.

Fulanin sun ce ba za su iya kiyasce adadin wadanda suka jikkata ba, ko gidajen da aka kona ba, inda suka ce wasu mutane ma sun mutu a harin.

A cewar Fulanin, jami’an sun shiga yankunan inda suka fara harbin kan mai-uwa-da-wabi, tare da bude wuta a kan gidajensu da manyan bindigu, lamarin da ya janyo konewar gidajensu da dama.

Sai dai kuma, babban jami’in rundunar tsaron, Sitdang Mungak, ya karyata zargin tare da cewa labarin shadi fadi ne kawai.

 “Ban samu jin ta bakin jami’anmu ba da suke wajen dangane da wannan rahoton da ya shafi rundunar Rainbow na cewa sun kai wani hari.

Idan ma wani rahoto mara kan gado ya same ku, ba jami’anmu ba ne sam,” a cewarsa.

Sai dai kuma, shugaban kungiyar Fulani ta (MACBAN) a jihar, Nuru Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki kwararan matakan shawo ka lamarin don kar ya kazanta.

“Muna da kwarin gwiwar cewa gwamnatin jiha ba za ta iya shawo kan wannan matsalar ba. Jami’an rundunar Rainbow da ‘yan daba suke jagoranta sun kona gidaje, kuma asalin manufarsu shi ne su fitar da mu daga Filato gaba daya.

“Kafin wannan rikicin na yau, mambobinmu da suke Sarpal, Kombun, Rinago, Dtmirle, Kangang, Aloghom, Fongon, Bongangida, Luggere, Gaude, Jwaksham, Borwa, Luggadimesa, Tidiw, da wasu wuraren su ma an kona musu muhallai. Kan hakan, muna kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ceto mu daga wannan halin da muke ciki,” kamar yadda ya shaida.

Isa Ibrahim Jamo, daya ne daga cikin al’ummar yankin da lamarin ya shafa, ya zargi jami’an da kona gidaje a Changal, Kombili, Lamor, Washina, Gayam, Anguwan Baraya, Bibim da wasu yankuna na Jannaret.

“Kadarorinmu da suka hada da kayan sawa, katifu, takin noma, abinci dukka sun kone. Mata da yara sun gudu zuwa kauyukan Gindiri da Kasuwan Ali domin fargabar abin da ka iya sake faruwa,” Jamo ya shaida.

Sai dai mazauna Mwaghabul ‘yan asalin Karamar Hukumar Mangu sun zargi Fulani da cewa suna ta kokarin mayar musu da muhallai wuraren kiwo a kokarinsu na mamaye gonakan yankin.

Kungiyar ‘yan kabilar ta kuma karyata zargin da Fulani suka yi na cewa jami’an rundunar Rainbow ta kai musu hari tare da kona wa mambobinsu wurare.

Shugaban kungiyar ci gaban Mwaghabul (MDA), Chief Joseph Gwankat, ya ce, “Mun fito ne domin mu shaida muku hakikanin abubuwan da suke faruwa da muhallanmu. Wasu ‘yan ta’adda na kai hare-hare a Mwaghabul da wasu sassan karamar hukumar Mangu.

“Al’ummar Mwaghabul mutane ne masu son zaman lafiya kuma suna zaune da makwabtansu lafiya. Kafin kokarin da Fulani suka fara yi na kutso kai suna so su mamaye mana wurare.

“Hare-haren da Fulani suke kawo mana ya fara ne tun a watan Afrilu har zuwa yanzu, da farko lamuran sun fara ne da garkuwa da mutane, lalata gonaki da wasu matsaloli daga baya lamarin ya zama kaddamar da hare-hare.”

“Abin takaici, wadanda suke kashe mu, su kashe mana jama’a su ne kuma suke ta korafin wai ana kona musu muhallai.

“A gundumar Bwai garuruwan da suka kunshi: Murish, Dungmunan, Kubat, Tim Naanle, Pil, Fungzai, Manja, da Chisum an kashe mutum 70.

“A gundumar Kombun: Fungkipang, Nting an kashe mutum 5. Gundumar Mangu a garuruwan da suka shafi: Jwaktumbi, Kantoma, Mangul, Alohom 1, Alohom 2, Gongon, Dan Hausa, Kikyau 1 da 2, Gudum, Tyop, Kwaskipanleng, Gaude, Bure, da Ntam, mutum 70 nan ma aka kashe.

“Gundumar Panyam: Changal, Kombili, Washna, Jwak Chom, Larkas, Fushi, Kwahas, Dangdai, Atuhun, Adep, Ajing, Daika, Dikong, Lakopal, Kogul, da Niyes, an kashe mutane.

Haka nan a gundumar Pushit: Lakasi, Gwet mutum 2, Gwet mutum 1, Mutong, Keptul, Gung, Pyantuhul, Kus Hi, Nbwor, Bodni, Pwaskop, da Nten an kashe mutum 17. Gundumar Kerang: Konji, an kashe mutum 8,” kamar yadda ya shaida.

Zuwa cikin makon nan rahotanni sun tabbatar da cewa rikice-rikicen baya-bayan nan a Karamar Hukumar Mangu sun kara lakume rayukan mutane ciki har da yara kanana.

Wannan ya sa Kungiyar Dattawan Arewa, (ACF), da ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) da Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) suka Allah wadai da rikicin da ke faruwa a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato da wasu sassan Jihar Benue.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Farin Lamba da ke gundumar Jos ta Kudu a Jihar Filato a tare da kashe mutane takwas ciki har da wata jaririwa ‘yar wata takwas.

Kamar yadda jami’in watsa labarai na kungiyar matasan Berom, ‘Berom Youth Moulders’, Rwang Tengwong, ya ce, maharan sun farmaki jama’a ne a lokacin da suke tsaka da bacci.

Ya ce, masu kisan sun zo ne cikin mota kawai suka bude wuta kan jama’a.

Kazalika, an kai harin ne kwana guda bayan kaddamar da wani hari a kauyen Sabon Gari da aka ba da labarin cewa mutane da dama sun rasa rayukansu kuma an kona gidaje da dama.

Haka zancen yake a wasu kauyuka da dama da aka samu labarin faruwar hare-haren.

Kungiyar Dattawan Arewa ta ce lokaci ya yi da gwamnati za ta kawo karshen wadannan kashe-kashen da ake yi wa jama’a, inda ta nemi gwamnatin ta tilasta wa hukumomin tsaro daukar kwararan matakan shawo kan matsalar.

Murtala Aliyu, Sakatare Janar na Kungiyar ACF, ya nuna damuwarsu da kashe-kashen da ke faruwa a Filato.

Ya ce, kamata ya yi gwamnatoci a dukkanin matakai su dauki matakan da suka dace domin kawo karshen lamarin ba ma kawai a zallar Filato ba har ma da sauran wuraren da ake fama da matsalar tsaro.

Aliyu ya ce, “Abin takaici, an san Mangu ta kasance waje ne mai cike da zaman lafiya. Ko a rikice-rikicen baya-bayan da aka yi a Filato ba su shafi yankin ba, amma a yanzu abin da ke faruwa abin damuwa ne matuka gaya. Don haka muna fatan hukumomin tsaro za su yi kokarin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yanki.”

Kazalika, kungiyar ta nemi al’ummar yankin da shugabanni da su yi kokarin dawo da martabar zaman lafiya a yankunansu.

Aliyu ya ce Jihar Filato jiha ce mai albarkatun tattalin arziki a Arewacin kasar nan, ya nuna cewa rikice-rikicen za su janyo koma baya ne ga tattalin arziki.

A sanarwar da ya fitar, shugaban JNI kuma Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna II, ya yi fatan cewa za a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin Mangu.

Sarkin ya nemi hukumomin tsaro da su yi dukkanin abubuwan da suka dace wajen hana sa shinge a kan hanyoyi a Mangu, yana mai cewa wasu fasinjoji da dama an kashe su ne sakamakon tare hanyoyin.

“Yana da kyau a irin wannan lokacin jami’an tsaro su nuna kwarewa sosai wajen kula da cunkoso domin bai wa matafiya damar wucewa lafiya.”

Kazalika, JNI ta nemi Gwamnatin Jihar Filato da ta tabbatar ta sauke nauyinta na kare rayuka da dukiyar jama’a. Sannan ta bukaci jama’a da su kara rungumar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ta nan ne rayuwa ta ke inganta.

A nata bangaren, CAN ta ce gwamnatin jihar ta magance matsalar kawai ba tare wani bata lokaci ba.

Shugaban kungiyar ta CAN reshen Jihar Filato, Rabaran Fr. Polycarp Lubo, ya ce, tsawon shekaru gwamnati ta san matsalar yanzu lokaci ne kawai da za a yi gyara.

Ya ce ba wani dalilin da za a cigaba da fuskantar irin wannan rikicin a gabar da za a iya shawo kansa cikin kankani lokaci.

Ya ce wasu da ba su san hawa da saukar ba su ne ake dora wa alhakin kai hari da ramuwar gayya.

Ya ce sun gano an biya wasu Naira 50,000 domin su tayar da wannan fitinar, kana ya nemi a bankado su tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Ita kuwa rundunar sojoji ta ‘Operation Safe Haben (OPSH)’ ta tabbatar da azamarta ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Filato har ma ta ce zuwa yanzu ta kwato bindigogi kirar gida guda biyar a wasu yankunan Mangu.

Kyaftin Oya James, jami’in yada labarai na rundunar, ya shaida cewa, sun kwato albarusai da dama a yayin samamen da suke yi a yankunan da ake samun rikice-rikicen.

Ya ce Babban Kwamandan runduna ta 3 ta sojojin Nijeriya, Manjo Janar Abdulsalami Abubakar, kuma da yake matsayin Kwamandan runduna ta musamman ta OPSH, ya ziyarci yankin tare da daukar kwararan matakan maido da zaman lafiya.

Rikice-rikicen sun sanya hukumar kula da shirin matasa ‘yan bautar kasa (NYSC) ta sanar da sauya wa sansanin horar da matasan matsuguni daga Karamar Hukumar Mangu zuwa Jos ta Kudu domin kiyaye rayukan wadanda ake turowa jihar.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa ta shafinta na facebook, NYSC ta ce “Ana sanar da matasa masu shirin bauta wa kasa kashi na biyu, rukunin farko, cewar an sauya inda za a yi musu horo daga sansanin horar da matasa na Mangu, zuwa gidauniyar Waye, da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu.”

Sanarwar ta bukaci matasan da su hallara a sabon adirenshi da aka bayar domin samun horo a kwanakin da aka ware.

A halin yanzu dai hankula sun fara kwanciya, sai dai har yanzu ana neman amsar wannan tambayar ta shin me ke faruwa a Filato, ganin kashe-kashen da ake yi na da tarihi ne tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999. Sai dai an samu sauki a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar da bai jima da sauka ba, Simon Bako Lalong duk da cewa a karshen mulkin nasa rikice-rikicen suka fara sake kunno kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here