Kotu ta ba DSS umarnin gaggauta sakin Emefiele

0
123

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin gaggauta sakin dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da ke tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS.

Kotun ta ce kamawa tare da tsare dakataccen gwamnan Babban Bankin da DSS ke yi ya saɓa wa doka.

Yayin da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bello Kawu ya ce kamawa da kuma bincikar Mista Emefiele, ya saɓa wa hukunci da kuma umarnin da wata kotun ta bayar na sakin sa.

Lauyan Emefiele, Peter Abang, ya nemi kotun da ta jingine sannan ta ayyana kamu tare da tsare shin da hukumar DSS ke yi a matsayin haramtacce.

Kasancewar a ranar 29 ga watan Disamban 2022 wata kotu ta dakatar da kama Mista Emefiele.

Aminiya ta ruwaito cewa a Alhamis din da ta gabata ce DSS ta ce ta gurfanar da Godwin Emefiele a gaban kotu.

Wannan ya biyo bayan umarnin da wata Babbar Kotu a Abuja ta bayar ranar Alhamis cewa ko dai DSS ta gurfanar da shi cikin mako guda ko kuma ta sake shi.

’Yan sa’o’i bayan wannan umarnin ne, kakakin DSS, Peter Afunanya ya ce an gurfanar da Emefiele bisa biyayya ga umarnin kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here