Kotu ta wanke dan wasa Mendy daga zargin laifin fyade

0
117

An wanke dan wasan Manchester City, Benjamin Mendy daga laifin yi wa wata mata fyade.

An zargi matashin mai shekaru 28 da kai wa wata mata ‘yar shekara 24 hari a gidansa da ke Motram St Andrew, Cheshire a watan Oktoban shekarar 2020.

An kuma zargin Mista Mendy da yunkurin yi wa wata mata fyade, mai shekaru 29.

Hakan na zuwa ne bayan da aka wanke shi daga laifukan fyade shida a wata shari’a da aka yi a baya a watan Janairu.

Dan wasan dan kasar Faransa, ya barke da kuka yayin da alkalin kotun ya karanta hukuncin da ba shi da laifi bayan shari’ar da aka shafe mako uku ana yi a kotun Chester Crown da ke Ingila.

Alkalan shari’ar maza shida da mata shida sun tattauna na tsawon awanni uku da mintuna 15 kafin su cimma matsaya.

Alkali Steven Everett, ya ce ana iya sallamar Mendy daga tashar jirgin ruwa da yake tsare.

Dan wasan wanda kwantiraginsa da Manchester City ya kare a wannan watan, an wanke shi a shari’ar farko da ake yi masa na aikata laifuka shida na fyade.

Da kuma cin zarafi daya, wadanda suka shafi ‘yan mata ko matasa hudu.

Sai dai alkalan kotun sun kasa yanke hukunci kan laifuka biyu da suka hada da fyade da kuma yunkurin fyade, lamarin da ya sa aka sake gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here