Yan TikTok sun kai ziyarar hadin kai ga rundunar ‘yan sandan Kano

0
140

Wasu fitatun masu amfani da Tiktok a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya sun kai wa rundunar ‘yan sandan jihar ziyara inda suka ce a shirye suke su hada kai da jami’an tsaron don kawo gyara da zaman lafiya a jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matasan sun kai ziyarar ne a ranar Laraba ga kwamishina don bai wa rundunar ‘yan sanda gudunmowarsu da yunkurinsu na ganin cewa ta basirar da suke da ita sun taimaka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.

Cikin wadanda suka kai ziyarar neman yin aiki tare da rundunar ‘yansanda har da matashin nan Mubarak Isa Muhammad wanda wata kotun majistare ta taba tsare shi da abokin burminsa Nazifi Muhammad Bala bayan samun su da laifin bata sunan tsohon gwamna jihar Abdullahi Umar Ganduje.

A bidiyon da rundunar ‘yan sandan ta wallafa, an ga matasa shida zaune a kujeru tare da SP Kiyawa, inda aka bai wa kowanne damar yin bayani kan dalilan da suke so su hada kai da ‘yan sanda don kawo gyara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here