Mamakon ambaliyar ruwa ya kashe mutane 22 a Koriya ta Kudu

0
168

Akalla mutane 22 ne suka mutu yayin da wasu 14 suka bace a Koriya ta Kudu, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa.

Kamar yadda jami’ai suka bayyana a a wannan Asabar, inda aka ba da umarnin wasu dubbai da su kauracewa gidajensu.

Galibin wadanda abin ya shafa cikinsu harda mutun 16 da suka mutu da kuma tara suka bace, sun fito ne daga lardin Gyeongsang ta Arewa, sakamakon zabtarewar kasa a yankin mai tsaunuka da ya mamaye gidaje da mutane a ciki.

Ma’aikatar cikin gidan Koriya ta Kudu tace sama da mazauna yankin Goesan ta tsakiya 6,400 ne aka bukaci su fice tun da sanyin safiyar wannan Asabar, yayin da madatsar ruwa ta Goesan ta batse tare da mamaye kauyukan da ke kusa.

Koriya ta Kudu dai tana cikin tsakiyar lokacin damina kuma an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin kwanaki ukun da suka gabata, lamarin da ya haifar da ambaliya da zabtarewar kasa, wanda ya haifar da cikar wani babban dam din Goesan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here