Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci a matsayin martani ga hauhawar farashin abinci a kasar.
Dele Alake, mashawarcin shugaban ƙasar kan ayyuka na musamman ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci, kuma a yayin da ake ci gaba da kokawa, gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.
Me dokar ta-É“aci kan samar da abinci ke nufi, da tasirinta?
Da yake magana da BBC, masanin tattalin arzikin Najeriya, Bismarck Rewane ya ce ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci na nufin gwamnati ta gano kuma ta amince da lamarin hauhawar farashin kayayyakin abinci wanda ya yi muni da kuma daukar matakan warware su.
“Dokar ta-baci kan samar da abinci wani yanayi ne wanda ke buÆ™atar matakan warwarewa ta gaggawa. Don haka ana ayyana dokar ta-baci a kan samar da abinci saboda hauhawar farashin kayan abinci, hanyar samun kayan abinci ya ragu” in ji shi.
Masanin tattalin arzikin ya ce farashin canjin kudi a halin yanzu zai yi tasiri sosai kan sa hannun gwamnatin tarayya a kan samar da abinci.
Ya shaida wa BBC cewa “hawa ko saukar darajar Naira shi ne babban matakin da zai fi shafar farashin kayayyaki a kasuwannin Najeriya.”
Da yake magana a kan yadda gwamnati za ta iya samun nasara tare da bayar da tallafi, dole ne gwamnati ta jagoranci hanyar takaita wuce gona da iri da É“angaren kashe kuÉ—i.
Shi ma da yake magana da BBC, wani mai sharhi kan harkokin zuba jari, Victor Aluiyi ya yi imanin cewa idan ƙasa kamar Najeriya za ta yaƙi matsalar ƙarancin abinci yadda ya kamata, to akwai buƙatar sai ta ci nasara wajen yaƙi a kan rashin tsaro.
Ya ce tallafin gwamnatin tarayya ba zai taɓa yin tasiri ba idan har an bar rashin tsaro ya ci gaba da munana a yankin arewacin ƙasar.
Sauran masana sun goyi bayan ra’ayin Aluyi, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta yi alÆ™awarin shigar da tsarin tsaro don kare gonaki da manoma
saboda su iya komawa gonakinsu ba tare a wnai fargabar kai musu hari ba.
Aluyi ya ce Æ´an Najeriya su yi tsammanin samun sauki da gyara a farashin abinci a makonni masu zuwa.
“Ƴan Najeriya su yi tsammanin samun saukin a kan farashin abinci a nan gaba, ba lalle saukin ya zo nan da nan ba, watakila nan da makonni biyu masu zuwa farashin abincin zai iya sauka kaÉ—an.” Aluyi ya shaida wa BBC.