PSG za ta yi wa Bayern Munich yankan-baya

0
115

Paris Saint Germain na neman yi wa Bayern Munich yankan-baya a zawarcin Harry Kane daga Tottenham. (Independent)

Ita kuwa Manchester City ta kwallafa ranta a kan dan bayan Bayern Munich Benjamin Pavard, dan Faransa a matsayin wanda ta fi son saye idan dan bayan Ingila Kyle Walker, ya koma wajen zakarun na Jamus. (Guardian)

Sai dai kuma, Cityn na son Walker din ya sanya hannu a kwantiragin tsawaita zamansa da wata 12 yayin da Juventus ma ke sonshi bayan Bayern. (Mail)

Marseille na kokarin sayen Pierre-Emerick Aubameyang, daga Chelsea. (Relevo)

Haka kuma Marseille din na fatan sayen Iliman Ndiaye bayan da kungiyar ta cimma yarjejeniyar shekara biyar da dan gaban na Senegal mai shekara 23, to amma kuma har yanzu kungiyar ta Faransa ba ta gabatar da bukatarta ga Sheffield United ba. (L’Equipe)

Liverpool za ta duba yuwuwar shiga gogayyar sayen dan wasan tsakiya na Brighton Moises Caicedo na Ecuador mai shekara 21, idan Jordan Henderson da Fabinho suka tafi Saudiyya. (Talksport)

Ana sa ran Liverpool din ta sayar wa Al Ettifaq Henderson a kan kusan fam miliyan 10. (Football Insider)

Fulham ta sake yin watsi da tayi na biyu daga kungiyar Al Hilal ta Saudiyya a kan dan wasanta na Serbia Aleksandar Mitrovic. (90min)

Ita kuwa Fulham din ta bi sahun West Ham a zawarcin James Ward-Prowse a bazaran nan, ko da yake kungiyar dan wasan na tsakiya dan Ingila Southampton ba ta samu wani tayi a kansa ba. (Football Insider)

PSG na son sayen dan gaban Najeriya Victor Osimhen, na Napoli amma ba don ta maye gurbin Kylian Mbappe ba sai dai don ta shawo kan dan gaban na Faransa ya kulla sabon kwantiragin ci gaba da zama a kungiyar. (Sport)

Aston Villa za ta saurari tayin sayen Lucas Digne, wanda ake ganin watakila Napoli ce za ta sayi dan bayan dan Faransa. (Mundo Deportivo)

Bayer Leverkusen ta gaya wa Aston Villa din cewa dole sai ta zaro kudin da ba ta taba sayen wani dan wasa da su ba a tarihi idan har tana son dan Faransa Moussa Diaby. (Talksport)

Brentford ta gabatar da tayin fam miliyan 13 a kan Habib Diallo na Strasbourg a kokarin da take yi na shan kan West Ham a kan dan gaban na Senegal striker (Football Insider)

Manchester United ta yi watsi da tayin farko daga Galatasaray ta Turkiyya a kan dan wasanta na tsakiya Fred na Brazil. (90min)

Barcelona ta karkata ga neman wani dan bayan daban kasancewar ba za ta iya ci gaba da neman Joao Cancelo ko da aro ba daga Manchester City. (Sport)

A kan hakan ne Barcelonan ke harin tsohon dan wasan Cityn na matasa Pablo Maffeo, dan Sifaniya mai shekara 26, a matsayin daya daga cikin zabinta to amma kuma Sevilla ma na son dan bayan na Real Mallorca. (TV3, da AS)

West Ham ta tuntubi Ajax a kan ko za ta sayar mata da dan wasanta na tsakiya Edson Alvarez, dan Mexico, wanda kungiyar ta Holland ke son fam miliyan 35 zuwa 40 a kan mai shekara 25 din. (Athletic)

Haka kuma Hammers din na kokarin sayen Denis Zakaria, mai shekara 26, daga Juventus, wadda take son yuro miliyan 20 a kan dan wasan na tsakiya na Switzerland. (Sky)

Dan wasan gaba na Nottingham Forest Sam Surridge, zai tafi Nashville SC a kan fam miliyan 5. (Athletic)

Luton na dab da kammala yarjejeniyar aron dan bayan Manchester City Issa Kabore na Burkina Faso mai shekara 22. (L’Equipe)

Fulham da Crystal Palace sun yi tuntuba a kan dan gaban Southampton Che Adams na Scotland. (Sky Sports)

An goge wani hoton bidiyo na atisayen ‘yan wasan Everton, wanda magoya bayan kungiyar suka ce a cikinsa ana jin ana ambato sunan dan wasan da kungiyar ke son saye nan gaba Jonny Evans na Leicester, dan bayan Arewacin Ireland mai shekara 35. (Mail)

Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Danny Drinkwater, ya ce yana son ya sake komawa Leicester, kasancewar ba shi da kungiya tun barinsa Chelsea a bazarar da ta wuce. (Sun)

Kungiyar Trapani da ke rukuni na hudu a Italiya na son daukar tsohon dan wasan gaba na gefe na Arsenal da Ivory Coast Gervinho, mai shekara 36, wanda ya yi kakar da ta wuce a kungiyar Aris ta Girka. (Calciomercato)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here