Rikicin APC: Makomar kujerar shugabanta na kasa, Abdullahi Adamu

0
115

Gabanin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na kasa da aka shirya gudanarwa a ranakun 18 da 19 ga watan Yuli, wani yanayi na nuna rashin tabbas game da makomar kujerar shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Adamu.

Kamar yadda ya taba faruwa da tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole.

Adamu wanda ya zama shugaban APC na kasa a yayin gangamin wani taron jam’iyyar na kasa da kwamitin rikon kwarya da gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shirya a dandalin ‘Eagles Skuare’ da ke Abuja a watan Maris ta 2022, yana fama da matsin lamba kan ya ajiye mukaminsa bisa zarginsa da ake yi na wawushe kudaden jam’iyya ba bisa ka’ida ba.

Tsohon gwamnan na Jihar Nasarawa, Adamu ya samu goyon bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma a dalilin haka ne aka bukaci sauran masu neman takarar shugabancin jam’iyyar su janye masa.

Sai dai tun a farkon wa’adinsa na shekaru hudu a kan kujerar shugabancin jam’iyyar ya hadu tarnaki, a daidai lokacin da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi kira da ya yi murabus domin daidaita madafun iko ta bangaren addini.

A yayin da ake fargabar cewa kwamitin zartarwar jam’iyyar ta kasa, wadda shi ne na biyu mafi girma a jam’iyyar, zai iya goya masa baya sakamakon wasu zarge-zarge da suka shafi kudade da wasu abubuwa, kan haka Adamu ya gana da shugabannin jam’iyyar na jihohi a Abuja.

Ganawar ta gudana ce a shalkwatan jam’iyyar APC ta kasa a wani kokarin da shugaban jam’iyyar yake yi na neman goyon baya daga wurin shugabannin jam’iyyar na jihohi gabannin taron kwamitin zartarwar na kasa.

Idan za a iya tuna shugabannin jam’iyyar APC na jihohi dukkansu mambobin kwamitin zartarwa ne kuma suna iya kada kuri’ar rashin amincewa da shugaban.

Wani dan jam’iyyar APC na kasa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Babu wanda ya san abin da zai faru. Akwai mutanen da ba sa son salon shugabancin Adamu, akwai kuma masu rura wutar rikici da rashin jituwa a cikin jam’iyyar.

“A wancan lokacin, Adamu bai goyi bayan Tinubu ba, amma muka yi galaba a kansa, saboda mun ci zabe kuma lokaci ya yi da za mu hada kan jam’iyyar, sannan kuma wannan lokaci ne da za mu hada kan kasar nan.

“Tinubu ba ya tunanin korar Adamu a yanzu saboda ya yi wuri da yawa. Adamu zai iya yin murabus da kansa idan har ya ci gaba da samun matsin lamba.

“Idan Tinubu ya ga dama zai iya kula da sha’anin jam’iyyar, Adamu ba zai iya yin komai ba. Idan Tinubu ya yanke shawarar amsar ragamar shugabancin jam’iyyar, Adamu zai iya karbar umarni ne kawai daga gare shi. Don haka ba za a sami rikicin tsige Adamu ba.”

Wata majiyar ta ce da a ce za a tsige Adamu, da Tinubu bai nada tsohon gwamnan Jihar Benuwai, Sanata George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya ba.

Majiyar ta kara da cewa nadin Akume manuniyace ba za a tsige Adamu ba a yanzu.

Ta ce, “Siyasa ‘yar lissafi ce. Wani lokaci a yi nasara, sannan wani lokaci a samu rashin nasara.

“Duba da cewa da ba a nada Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya ba, da an ba shi matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa idan an tsige Adamu a lokacin taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

“Idan za a iya tuna, shugaban kasa ne kawai zai iya tsige shi ko ya yi murabus. Idan shugaban kasa ba ya bukatarsa, yana da ikon tara mambobin kwamitin zartarwa su jefa kuri’ar rashin amincewa.”

Idan dai za a iya tunawa, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a yankin Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman, ya bukaci Adamu ya yi murabus domin wani kirista ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron da Adamu, shugaban jam’iyyar na Jihar Kuros Riba kuma mukaddashin sakataren kungiyar shugabannin APC, Alphonsus Oga, ya ce kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar APC ya gayyace su domin gudanar da taron.

Sai dai ya musanta duk wani nau’i na rikici a jam’iyyar a matsayin dalilin dage taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Ya ce, “Kamar yadda kuka sani, tun bayan zaben da muka yi nasara, ba mu samu damar ganawa da shugabanninmu da shugabanmu na kasa da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ba.

“Mun samu damar gudanar da taron da aka shirya ne bisa gayyatar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya aika mana, kuma muna farin cikin sanar da ku cewa wannan wata dama ce ga shugabannin jam’iyyar APC na jihohi domin taya murna ga shugaban jam’iyyarmu mai girma, Sanata Abdullahi Adamu da tawagarsa masu himma wajen gudanar da aiki tukuru da suke yi.”

Da aka tambaye shi ko an dage taron na kwamitin zartarwa ne saboda sabon rikicin da ya kunno kai, Oga ya ce, “Wannan lokaci ne na jita-jita da zage-zage za su karu, amma jam’iyya APC a dunkule take, kuma mun sake haduwa ne domin bayar da goyon baya ga shugabanmu na kasa kuma mambobin kwamitin gudanarwa.

Da yake jawabi yayin bude taron, Adamu ya roki Shugaba Tinubu ya karfafa jam’iyyar.

Ya ce, “Muna fata tare da gudanar da addu’o’i cewa mai girma shugaban kasa ya yi aiki kafada da kafada da mu wajen karfafa dangantakar jam’iyyar a jihohi da ma kasa baki daya don samun wata sabuwar gwamnati nan gaba.

“Wadannan su ne muhimman batutuwan da muke fatan cimmawa tare da ku a yayin wannan taron.

“Mun yi tunanin cewa taron da muka yi da ku a matsayinku na shugabannin da ke da alhaki, ba shakka gwamnonin su ne jagororin jam’iyyarmu a jihohi, amma kuna tafiyar da jam’iyyar a kullum da kyakkyawar fahimtar juna a tsakaninku da gwamnoni da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa kamar yadda aka saba wajen inganta shugabancin da muke son yi wa jam’iyyar.”

Adamu ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta lashe zaben gwamnonin jihohin Bayelsa, Kogi da Imo da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here