Shin ko kun san nawa ne makudan kudin da ‘yan majalisa ke karba a duk wata?

0
142

Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da cewa kowanne dan majalisa yana karbar fiye da N13.5m a matsayin kudin gudanarwarsa duk wata.

Ta bayyana haka ne bayan daya daga cikin ‘yan majalisar, Sanata Shehu Sani, ya shaida wa wata kafar watsa labarai cewa kowannensu yana karbar N13.5m a matsayin kudin gudanarwarsa duk wata.

A cewar dan majalisar, “Baya ga wadannan kudade, kowanne dan majalisa yana karbar N700,000 a matsayin albashinsa na wata ban da sauran alawus-alawus da ake ba mu.”

Wannan tonon silili da Sanata Shehu Sani ya yi wa ‘yan uwansa ya sa mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Sahabi Ya’u fitar da sanarwar da ke tabbatar da kalaman takwaransa.

“Sanata Shehu Sani bai fadi wani sabon abu ba game da albashi da sauran kudin da ake gudanar da aikin dan majalisar majalisar saboda da ma wadannan bayanai suna cikin kasafin kudin majalisar dokokin tarayya, wanda kowa ya sani,” in ji sanarwar da Sanata Ya’u ya fitar.

Sanarwar da ya fitar ta zo ne sakamakon sukar da ‘yan majalisar ke sha a wurin ‘yan Najeriya wadanda ke ganin ‘yan majalisar na karbar makudan kudi amma babu abin da suke tsinanawa.

A baya dai an sha yin kira ga ‘yan majalisar su bayyana albashin da sauran kudaden da suke karbar amma suka ki.

Wannan lamari na faruwa ne a lokacin da ‘yan kasar ke fama da matsanancin talauci sakamakon tashin kayan masarufi da tsadar rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here