‘Yan sanda sun kama gawurtattun masu ‘satar mutane’ 7 a Bauchi

0
165

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Bauchi ta ce ta kama mutum bakwai wadanda ake zargin gawurtattun masu garkuwa da mutane ne da kuma kwato makamai daga wurinsu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce binciken wucin gadin da ta yi ya nuna cewa mutanen su ne suka addabi jama’ar yankin Karamar Hukumar Alkaleri.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, kungiyar mafarauta kuma masu aikin sa kai da hadin gwiwar ‘yan sandan jihar suka kai wani samame a wasu sansanonin masu garkuwa da mutanen.

Sanarwar ta ce wuraren da aka kai samamen sun hada da kauyen Babarko da ke gundumar Pali da kuma kauyukan Yalo da Karekare da Digare da Papa da ke gundumar Gwana.

Mutum bakwai wadanda ake zargin da garkuwa da mutane sun hada da: Isah Gambo mai shekara 25 da Hamza Ali mai shekara 26 da Ali Isyaku mai shekara 27 da Danlami Isyaku mai shekara 30.

Sauran sun hada da Abubakar Isyaku mai shekara 25 da Adamu Alh. Lado mai shekara 30 da Usman Dan Asibi mai shekara 30 wanda aka fi sani da Na Mansur.

Rundunar ‘yan sandan ta ce duka mutanen da ta kama sun fito ne daga kauyukan Papa da Yalo.

Haka kuma ‘yan sandan sun samu nasarar gano makamai a mabuyar wadanda ake zargi da garkuwa da mutanen.

Makaman sun hada da bindiga kirar pistol ta gargajiya mai sarrafa kanta guda daya da kuma bindiga kirar AK- 47 ta gargajiya guda daya.

Haka kuma akwai kuma akwai wata bindiga kirar pistol ta gargajiya guda daya da kuma bindiga kirar pump action ta gargajiya daya.

Rundunar ta ce a yayin binciken da ta gudanar, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma za ta gurfanar da su gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here