Ba kure mutane nake yi a shirin da nake gabatarwa ba – Hadiza Gabon

0
246
Gabon's Room Talk Show

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood a Nijeriya Hadiza Aliyu Gabon ta ce masu zarginta da cewa tana yi wa bakin da take gayyata tambayar kure ba su fahimci yadda tsarin aikin yake ba ne.

Gabon ta fadi hakan ne a hirarta da TRT Afrika, wanda shi ne karo na farko da ta yi hira da ‘yan jarida kan shirin nata na Gabon’s Room Talk Show.

Tun bayan da ta fara gabatar da shirin dai Hadiza ta gayyaci mutane daban-daban daga kan ‘yan fim zuwa masu shiryawa d aba da umarni har ma da mawaka, lamarin da ya dinga jawo ce-ce-ku-ce a lokuta daban-daban kan irin yadda take wa bakin tambayoyi.

Daga cikin wadanda suka fi jan hankalin mutane da jan tsokaci har da na Rakiya Moussa Poussi, wacce ta ba da labarin soyayyarta da wani fitaccen mawaki da ba ta ambaci sunansa ba, abin da har ya jawo ta dinga kuka yayin amsa tambayoyin Hadiza.

Sannan akwai na wani furodusa El Mu’az wanda shi ma wata tambaya da ta yi mas a kan “soyayyarsa da jaruma Hannatu Bashir” ta tayar da kura sosai a kafofin sadarwa a arewacin Nijeriya.

Wasu sun yi ta zargin Hadiza ta cewa ta shiga aikin jarida bayan ba aikinta ba ne kuma ba ta da horo a kansa, “shi ya sa take tambayoyin suka zam tamkar kure mutum ne.”

Sai dai Gabon ta shaida wa TRT Afrika cewa wannan shiri nata nadarsa ake yi ba kai tsaye ake yada shi ba, don haka duk bakon da ta kawo yana da ikon idan an yi masa tambayar da ba ya son amsata ya ce ba zai amsa ba.

“Ka san duk muutmin da za ka masa tambaya, yana da damar ya ce ba zai amsa ba, kuma ba ka isa ka tilasta shi ba,” in ji ta.

Da aka tambaye ta ko ta sanar da bakin nata tambayoyin da za ta yi musu kafin a fara nadar shirin, sai ta ce “yanzu misali idan na gaya muku sirrin hakan ai kun karya min irlina,” ta fada cikin dariya.

“Abin da nake so mutane su gane shi ne cewa duk wanda ya zo a matsayin bakon shirin to ya san abin da ya sa ya zo kuma ya san tambayoyin da za a yi masa tun da ya ga na wasu,” ta jaddada.

Kazalika tauraruwar a Kannywood ta yi magana kan masu sukarta da shiga aikin jarida bayan ba aikinta ba ne, inda ta ce tana samun goyon baya daga wasu manyan ‘yan jaridar ma da dama.

“Ai ina da yayye da yawa ‘yan jarida duk suna nan, da wadanda a ban taba haduwa da su ba da suke ba ni shawarwari a bayan fage, kuma ina godiya gare su,

“Sauran ‘yan jarida kuma da suke jin haushi don Allah ku yi hakuri, za mu gyara,” Gabon ta fada.

Hadiza ta ce babban abin da ya ja hankalinta ta fara wannan shiri nata na Gabon’s Room Talk Show shi ne kallon shirye-shirye irin na su Steve Harvey da Oprah da Ellen Degeneres da sauran su.

“Suna burge ni sosai. Wasu lokutan idan wani ya zo yana fadar labarinsa a shirye=shiryen nasu sai ka ji tamkar da kai ake yi.”

TRT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here