DA DUMI-DUMI: Farashin man fetur ya tashi zuwa Naira 617 akan kowace lita

0
172
man fetur
man fetur

Farashin Man Fetur ya karu zuwa kusan Naira 617 a kowace lita, kamar yadda Aminiya ta tabbatar.

Ziyarar da wannan dan jarida ya kai wani gidan mai na NNPC da ke tsakiyar Abuja ya tabbatar da cewa yanzu an daidaita farashin man daga Naira 539 zuwa N617 kowace lita.

Wani abokin ciniki da ya tabbatar wa Aminiya haka ya ce, “Gaskiya ne, na saya kan Naira 617 kan kowace lita.”

Har yanzu dai ba a iya gano dalilin da ya sa ba, amma bai rasa nasaba da hasashen da ‘yan kasuwar man suka yi na cewa farashin mai zai kai Naira 700 kan kowace lita nan ba da jimawa ba.

Aminiya ta ruwaito cewa Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NDMPRA) ba ta ce uffan ba game da binciken ta har zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto.

Cikakkun bayanai na tafe…..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here