Hukumar Kwastam ta kama muggan makamai a Legas

0
150

Hukumar hana fasa-kwauri ta Nijeriya wato kwastam ta ce ta kama jakunkuna dauke da manyan makamai da alburusai a birnin Legas da ke kudancin kasar.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada ranar Talata.

Sanarwar, wadda kakakin hukumar ya sanya wa hannu, ta ce “hukumar Kwastam ta kama bindigogi talatin da dayada alburusai da aka boye a wasu duro-duro da buhunan gawayi a makonni biyu na watan Yulin 2023.”

Kazalika hukumar ta ce ta kama mutum biyu da ake zargi hannu da wannan aiki.

Sanarwar ta ambato shugaban riko na hukumar Bashir Adewale Adeniyi yana sanar da hakan a lokacin ziyarar da ya kai birnin na Legas ranar Litinin.

Ya bayyana cewa sashen leken asiri na Kwastam ya hada gwiwa da rundunar ‘yan sanda da jami’an hukumar leken asiri ta DSS da na hukumar hana sha da fataucin kwaya NDLEA wajen yin kamen.

Lamarin ya faru ne a tashar jiragen ruwa ta Ports & Terminal Multiservices Limited, inda ta “ta bankado manyan makamai masu hatsarin gaske guda goma da alburusai da aka boye a duro na roba.”

Hakan na faru ne a yayin da su ma sojojin Nijeriya suka kama mota dauke da fakiti 720 na harsasai sannan suka kama wani gungun masu safarar makamai a hanyarsu ta zuwa Anambra.

Nijeriya ta dade tana fama da rashin tsaro wanda ake alakantawa da yawaitar yaduwar makamai a hannun ‘yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here