Kungiyar kwadago ta yi watsi da shirin Tinubu na biyan ‘yan Najeriya N8,000

0
131
Kungiyar Kwadago
Kungiyar Kwadago

Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi Allah-wadai da matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman amincewar majalisar dokoki don karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin Duniya da nufin aiwatar da shirin da ta kira na bogi don rage raɗaɗin ƙarin farashin man fetur da aka yi babu lissafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce, “Shawarar biyan naira 8,000 ga magidanta miliyan 12 mafiya talauci a Najeriya tsawon wata shida cin mutunci ne da kuma ba’a ga haÆ™uri da imani da muke da shi a kan tattaunawa da gwamnati.”

“Rashin tunani ne gwamnatin da ta haddasa tsananin wahala a kan mutane cikin Æ™asa da wata biyu da hawanta mulki, sannan ta zo ta kawo wani Æ™uduri wanda Æ™arara zai saka wa masu kuÉ—i da ke riÆ™e da muÆ™aman gwamnati, ba tare da duba halin da talakawa ke ciki ba.”

“Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa ‘yan Najeriya, su kuma masu kuÉ—i su Æ™ara kuÉ—ancewa.”

NLC ta ce ba za a lamunci waÉ—annan Æ™udurori ga ma’aikatan Najeriya ba kuma matakin ya fi kama da kama-karya don haka ya saÉ“a da tsarin dimokraÉ—iyya.

“Muna nanata cewa ba mu da Æ™warin gwiwa kan hanyar da aka bi aka tattara bayanan da ba sa canzawa na gidajen mutanen da suka fi talauci su miliyan 12, sannan ba mu da Æ™warin gwiwa a kan tsare-tsare da za su bi wajen raba wannan kuÉ—i.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here