Lauyoyi 60 sun yi karar DSS kan rashin sakin Emefiele

0
124

Akalla lauyoyi 60 ne suka garzaya wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya domin shigar da kara kan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) saboda kin sakin Emefiele.

Lauyoyin sun ce karar na da nasaba da cin zarafin wasu hukunce-hukuncen da kotun ta umarci hukumar ta saki tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Lauyoyin da Mista Maxwell Opara da Ahmed Tijani suka jagoranta, sun roki kotun da ta kai wasu manyan jami’an DSS gidan yari har sai an sallami Emefiele.

Lauyoyin sun ce bisa hukunci da mai shari’a M. A. Hassan da Hamza Muazu da kuma mai shari’a Bello Kawu suka yanke, ya kamata Darakta-Janar na DSS, Yusuf Magaji Bishi, ya saki Emefiele.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan shigar da karar, Opara ya ce kungiyar za ta bi diddigin lamarin har zuwa karshe sannan kuma ta tabbatar da cewa an tura Darakta-Janar na DSS, Bichi zuwa gidan yari.

Ya ce hakan zai zama izina ga sauran shugabannin hukumomin tsaro na kin bin umarnin kotu.

Opara ya ce hukumar DSS ba ta da hurumi na tuhumar Emefiele da aikata munanan laifuka sai dai ta gabatar da shi a gaban kotu.

An jima ana tirka-tirka kan bukatar sakin Emefiele tun bayan da DSS ta cafke shi, bayan dakatar da shi daga CBN.

Ya shigar da kara inda ya nemi kotu ta tilasta DSS ta dakata daga tuhumarsa.

Kotun ta amince inda ta bukaci hukumar ta sake shi ko ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Sai dai duk da wancan umarni na kotu, DSS na ci gaba da tsare Emefiele a komarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here