Sarkin Bauchi ya jagoranci addu’ar rokon ruwa

0
176

Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, ya jagoranci dubban al’ummar musulmai wajen gabatar da sallar addu’ar rokon ruwa a fadin jihar. 

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa manoma a jihar musamman cikin masarautar Bauchi su na ta kokawa da rashin wadataccen ruwan sama da hakan ke barazana ga samun damina yadda gonakai ke bukata a wannan daminar na bana.

Masu addu’ar sun roki taimako da gudunmawar Allah da ya amince ruwan sama ya sauko wa al’ummar jihar musamman masarautar Bauchi don samun damina mai albarka.

Da yake jawabi a wajen salla mai raka biyu da addu’o’in neman ruwa da aka yi a babban masallacin Idi da ke Bauchi a ranar Talata, sarkin Bauchi Rilwanu Sulaiman ya bukaci al’umma da su kaurace wa dukkanin ayyukan sabon Allah da ka iya janyo fushin Allah.

A cewarsa, “Dole ne mu kauce wa dukkanin nau’ikan sabon Allah da suke janyo al’umma su kasa samun ni’imar Allah.”

Kazalika, ya bukaci jama’a da su cigaba da zama cikin kwanciyar hankali domin samun cigaba masu ma’ana a kowani lokaci.

A cewar Sarkin ta hanyar kyautata zaman lafiya, albarkatu da dama za su cigaba da zuwa ga al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here