Jama’a da dama a Najeriya sun wayi gari ba zato ba tsammani da karin farashin man fetur inda wasu gidajen mai a Abuja babban birnin kasar suke sayar da fetur din kan 617.
Hakan na nufin an samu karin naira 77 kan farashin da ake sayar da shi na 540 a wasu wurare.
Sai dai a cewar kamfanin mai na Nijeriya NNPCL, shugaban kamfanin Mele Kyari, ya dora alhakin karin farashin kan yanayin kasuwa.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai bayan ya tattauna da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Mista Kyari ya kara jaddada cewa ba karancin fetur din bane ya sa farashin ya karu sai dai yanayin kasuwa.
Tuni wasu gidajen mai da ke kwaryar birnin Abuja suka kara farashin litar mai a jikin injin din sayar da mai da kuma allon da ke dauke da farashi na gidan mai.
Karin farashin na zuwa ne kasa da wata biyu bayan farashin man ya karu daga 195 zuwa 540.
Dama a kwanakin baya an ta rade-radin cewa za a yi karin farashin na fetur, sai dai kungiyar dillalan man fetur din kasar ta fito ta nesantar da kanta daga hakan.
Ga dai yadda wasu ‘yan kasar ke korafi kan kadin kudin man: