Adadin masu siyan man fetur ya ragu sosai – NMDPRA

0
88

Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA), ta ce yawan man fetur da ake amfani da shi ya ragu matuka bayan cire tallafin da gwamnatin tarayya ta yi.

Adadin amfanin yau da kullun ya kai lita miliyan 46.38, ya ragu da lita miliyan 65 a kowace rana kafin a rage tallafin.

Farashin man fetur ya tashi zuwa Naira 617 a kowace lita a gidajen mai na Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) da ke Abuja.

Wannan ci gaban ya zo ne watanni bayan da kamfanin mai ya amince da sake duba farashin man fetur a fadin kasar nan.

Bayan wannan sanarwar, kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya umarci gidajen man da ke fadin Nijeriya da su sayar da mai tsakanin Naira 480 zuwa 570 kan kowace lita, kusan kashi 200 cikin 100 na farashin man fetur a kasa da N200.

Nan take hauhawar ta haifar da karin farashin sufuri da farashin kayayyaki da na ayyuka.

A gefe guda kuwa, shugaban hukumar NMDPRA, Ahmed Farouk yayin taron masu ruwa da tsaki da masu gudanar da ayyukan hakar mai da iskar gas a Legas, ya ce adadin ya nuna raguwar kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 a kowace rana, kafin a cire tallafin.

“Yawan man fetur da ake amfani da shi a kullum ya ragu sosai sabanin lita miliyan 65 da ake sha a kullum kafin a cire tallafin.”

Dangane da shigo da mai, Farouk ya ce sama da kamfanoni 56 ne suka nemi lasisin shigo da mai, yayin da 10 kacal suka yi alkawarin shigo da man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here