Hanyoyi uku na samun sauki daga radadin karin farashin fetur

0
130

A ranar Talata 18 ga watan Yuli ne aka wayi gari da karin farashin man fetur a Nijeriya inda jama’a ke ta kokawa dangane da hakan.

Tsadar rayuwa ta karu a kasar inda kwana guda kafin karin farashin fetur din hukumar kididdiga ta kasar ta fitar da sanarwar cewa an samu karuwar hauhawar farashi a kasar.

Bayan karin farashin da aka yi, kamfanin man fetur na kasar ya fito ya bayyana cewa kasuwa ce ta yi halinta sakamakon cire tallafin da aka yi.

‘Yan kasar dai na neman hanyoyin da za su bi domin rage radadi da kuma samun sauki. Ga wasu hanyoyi da za ku bi domin samun sauki a Nijeriya:

Duk abin da bai zama wajibi ba a dakatar da shi

Masana tattalin arziki irin su Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa domin jama’a su samu sauki, duk wani abin da bai zama dole ba, a dakatar shi.

Akwai abubuwa da dama wadanda rayuwa za ta ci gaba ko ba a yi su ba amma wasu jama’a na tilasta wa kansu kan dole sai sun yi.

Akwai jama’ar da ba su iya wata uku cif ba su sauya wayar salularsu ba, wanda hakan ba dole bane, haka kuma akwai wadanda ba su iya shekara guda da mota daya su ma sai sun yi kokarin canza ta.

Haka kuma akwai wadanda duk wata sai sun yi sabon dinki ko kuma yin wata hidima wadda ba dole bace.

Zuwa unguwa sai ya zama dole

A cewar masanin, akwai bukatar mutane su sauya yadda suke rayuwa musamman masu son zuwa unguwa a-kai-a-kai.

Ya bayyana cewa ko mene ne ya faru idan mutum ya tsara rayuwarsa, zai samu sauki.

“Mata masu son zuwa biki, za a je Zariya za a je Funtua za a je Abuja biki a kwashi ‘ya’ya. Duk wurin da bai zama dole ba, ba sai an je ba.

“Wadda za ki je wa biki idan abin da za ki taimake ta da shi za ki iya tura mata, Allah ya kawo sauki, kina gidanki za ki tura wa mace kudi, kudin ma sun fi mata sauki da amfani da ki je ki yini ki kwana ba wani abu za ki yi ba,” in ji shi.

Sa’annan su ma maza masu yawan zuwa unguwanni daban-daban da sunan hira a kullum, akwai bukatar su rage.

Rage almubazzaranci da takaita hidimomin gida

Akwai bukatar magidanta su hada kai da iyalansu domin nemar wa kai sauki inda hakan ya danganta da karfin tattalin arzikin mutum.

Mutane da dama suna almubazzaranci musamman wurin dafa abinci inda ake dafa abincin da sai dai a zubar, ko kuma barnata kayan hadin abinci kamar su man gyada wadanda su ma kayayyaki ne masu tsada.

Sa’annan makamashi iri daban-daban da ake amfani da su a gidaje kamar wutar lantarki da gas ko kalanzir ya kamata a san yadda ake amfani da su ba tare da an barnata su ba.

Akwai hidimomin gida na yau da kullum da dama wadanda ya kamata mutane su rage domin samun sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here