Messi na bukatar lokaci kafin ya saba da gasar MSL – Beckham

0
152

David Beckham na ganin Lionel Messi na bukatar karin lokacin kafin ya saba da sabuwar gasar Major League Soccer, duk da cewa yanayin wasan ya sha bamban da na wasan Turai.

Daya daga cikin mamallaka Inter Miami, Beckham, wanda tsohon dan wasan tsakiya ne na Manchester United da Real Madrid, ya je kallon Messi a lokacin da ya halarci atisayensa na farko a kulob din a ranar Talata bayan dan wasan ya saka hannu kan kwantiragi na shekara biyu da rabi.

Dan wasan tsakiya na Sifaniya Sergio Busquets wanda tsohon abokin wasan Messi ne tun daga Barcelona shi ma ya yi atisaye a filin kulob din bayan kulla yarjejeniya a ranar Asabar, tare da tsohon kocin Barcelona da Argentina Gerardo ‘Tata’ Ma rtino wanda shi ne ke horas da su.

“Duk yadda yake da kyau da karfi, Leo da Sergio na bukatar lokaci domin su saba koma dai mene ne,” kamar yadda Beckham ya bayyana.

“Za su iya ba ku mamaki, akwai yiwuwar mu iya samun nasara a kowane wasa, amma dole ne mu yi hakuri,” in ji shi.

Akwai bukatar magoya bayan Miami su nuna irin wannan hakuri a yayin wasan da za a buga a ranar Juma’a da kungiyar Mexico Cruz Azul, inda Beckham din ya bayyana cewa ba lallai bane dan wasan na Argentina ya fara.

“Leo zai buga wani bangare na wasan amma koci ne ke da wuka da nama kuma hakan ya dogara ne kan Leo idan ya ce a shirye yake domin mun san cewa ya shafe makonni da iyalansa amma yana kama da ya shirya kuma lafiyarsa kalau amma duk da haka yana bukatar lokaci ya saba,” in ji Beckham.

Beckham ne dan wasa mafi girma da ya koma gasar MLS a lokacin da ya saka hannu kan yarjejeniya da Galaxy a 2007 a lokacin da gasar League din ke da kungiyoyi 13 kacal idan aka kwatanta da 29 da ake da su a yanzu haka kuma a lokacin tsarin wasan bai kai na yanzu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here