Hisbah ta fara raba fom din auren zawarawa a Kano

0
145

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kafa kwamitoci guda biyu waɗanda za su yi aikin rabon fom da tantance lafiyar masu buƙatar shiga shirinta na auren zawarawa da ‘yan mata. 

Ta ce shirye-shiryen sun yi nisa, tun bayan samun amincewar gwamnatin Kano na gudanar da shirin auren zawarawa da ‘yan mata 1,800. 

Shugaban Hizba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce za a bai wa ƙananan hukumomin cikin birnin Kano takwas, gurbin mutum hamsin kowacce, yayin da ƙananan hukumomin wajen birni kuma za a ba su gurbin mutum 30. 

Fitaccen malamin ya ce idan mutum yana da sha’awar shiga shirin, da farko zai je ya karɓi fom. Sannan a cike bayanai muhimmai da hukumar Hizba take buƙata guda shida. 

“Na farko”, in ji Sheikh Daurawa, “mu san asalin mutum. Na biyu mu san sana’arsa, mu san halayensa, sannan mu tantance lafiyarsa.” 

“Sannan ya kawo mutum da za su ba da shaida a kansa cewa (shi) mutumin kirki ne. Sannan kuma ya zama mun samu cikakken bayani dangane da inda yake zama,” cewar shugaban na Hizba. 

Ya ce hukumarsu ba haɗa auren za ta yi ba, ga duk mai sha’awar shiga shirin zai karɓi fo ne bayan ya/ta daidaita da wanda yake/take son aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here