Gini ya rufta a Legas, ya hallaka mutum biyu

0
146

Yara biyu sun rasa rayukansu a wani gini da ya rufta a titin Ajao da ke unguwar Ikorodu a jihar Legas.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ta ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar.

“Yaran ‘yan shekara tara da kuma bakwai sun maƙale ne a lokacin da katangar gidan da ke makwaɓtaka da su ya faɗa kan gininsu a lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya,” in ji Kodinetan Hukumar NEMA a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, a cikin wata sanarwa. 

Hukumar ta ce ba a samu kai agajin gaggawa ba a kan lokaci don ceto rayukan yaran. 

Gidan talabijin nan Channels ya ruwaito cewa NEMA ta jajanta wa iyayen yaran da lamarin ya rutsa da su tare da addu’ar Allah ya basu ikon jure rashin. 

Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) ta je wurin da lamarin ya faru domin tantance lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here