Makiya Musulunci sun kona Alkur’ani mai girma a Denmark

0
203

Mambobin wata kungiya mai matukar nuna kiyayya ga Musulunci a Denmark sun kona Alkur’ani da tutar kasar Iraki a yayin da duniya take ci gaba da Allah wadai bisa kona littafin mai tsarki a Sweden.

‘Yan kungiyar mai suna Danske Patrioter sun kona Alkur’anin ne a wajen ofishin jakadancin Iraki da ke Copenhagen, babban birnin kasar ranar Juma’a.

Kazalika sun rike kwalaye da aka yi rubutu da ke zagin Musulunci da Musulmai, sannan suka fito da Alkur’ani mai tsari da tutar kasar Iraki suka kona su bisa kariyar ‘yan sanda, kamar yadda bidiyoyin da aka watsa a soshiyal midiya suka nuna.

‘Yan kungiyar sun ce sun dauki matakin ne domin mayar da martani ga harin da aka kai a ofishin jakadancin Sweden da ke birnin Bagadaza.

Ranar Alhamis da sassafe, dandazon masu zanga-zanga a Iraki sun cinna wuta a ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza don nuna fushinsu ga kona Alkur’ani da wani mutum mai suna Salwan Momika ya yi a Sweden ranar 28 ga watan Yuni daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar Layya.

Mutumin Kirista ne dan asalin Iraki wanda aka haifa a Sweden.

A gefe guda, Turkiyya ta bayar da umarnin a kamo mata dan siyasar nan na kasar Denmark Rasmus Paludan da mutum tara wadanda ake zargi da kona Alkur’ani a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Stockholm a watan Janairu, a cewar ministan Shari’ar Turkiyya.

“Ofishin Babban Mai Shigar da Kara ya bukaci a yi bincike mai zurfi domin gano wadanda ake zargi da kuma samo shaidun da suka nuna cewa an aikata wannan laifi,” in ji Ministan Shari’a Yilmaz Tunc.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here