Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin IPOB a Asaba

0
170

Rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya sun lalata sansanin ‘yan ungiyar awaren IPOB da takararta ta ESN a Asaba da ke jihar Delta.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce jami’anta sun kaddamar da samame kan sansanin ‘yan awaren da ke takiyar babban dajin Asaba da safiyar ranar Asabar, inda suka samu nasarar kwato makamai.

Sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar a lokacin samamen, inda daga bi-sani ‘yan bindigar suna gudu daga maÉ“oyar tasu.

Sanarwar ta ce sojojin sun kama daya daga cikin mayaÆ™an ‘yan awaren, tare da Æ™wato bindigogi biyar kirar AK-47, da manyan bindigogi masu sarrafa kansu uku. da wata Æ™irar G3 da Æ™amar bindiga guda.

Sauran abubuwan da dakarun sojin suka ƙwato, sun hadar da kwanson saka alburushi biyar, da gatari da kuma tutar kungiyar IPOB.

Babban hafsan sojin Æ™asa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yaba da namijin Æ™oÆ™arin da sojojin suka yi tare da sauran jami’an tsaro, a yunÆ™urinsu na kawar da ayyukan ‘yan bindigar da ke addabar yankin, tare da maido da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here