Tallafin N8,000 zai biya bukatun iyalai da dama – Gwamna Sule

0
147

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce tallafin N8,000 da Gwamnatin Tarayya ke kokarin rabawa domin rage radadin janye tallafin man fetur zai biya wa iyalai da dama bukatunsu.

Da yake zantawa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, Gwamna Sule ya ce Naira dubu takwas kudi masu yawan gaske ga iyalai da dama da ba sa iya samun wannan adadi a wata guda.

Ya yi tsokaci kan yadda gwamnatin da ta shude ta rika rabawa iyalai tallafin N5,000, lamarin da ya ce yunkurin da gwamnatin yanzu ke yi na raba N8,000 abun ma a yaba ne.

“Na yarda cewa akwai wadanda suke ganin N8,000 ba wasu kudade ba ne da suka taka kara suka karya, amma duk da haka a wurin wasu iyalan da ke cikin talauci kudin zai yi musu rana nesa ba kusa ba.”

Hausa24 ta ruwaito cewa a bayan nan ne dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sake nazari kan shirinsa na raba N8,000 ga matalauta domin rage radadin janye tallafin man fetur.

Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Dele Alake ya ce Tinubu ya sauya shawara kan shirin ne sanadiyyar sukan da yake sha daga ’yan Najeriya.

Lamarin na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawa ta sahale wa Gwamnatin Tarayya raba N8,000 ga matalauta miliyan 12 tsawon watanni shida domin rage radadin janye tallafin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here