A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano, ta tabbatar da barkewar cutar mashako wadda kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 25 a Jihar.
A wata sanarwa da Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ya fitar, ta ce alamomin cutar sun haɗa da zafin makogwaro da tari da yawan tufar da yawu da sauyawar murya da mura da warin baki da kuma shan wuya yayin numfashi.
Kwamishinan ya ce tuni aka kafa kwamitin gaggawa a jihar da ke tattaunawa kan yadda za a shawo kan cutar.
Tsanyawa ya ce a halin yanzu, tawagar sashen gaggawa, sun kaddamar da wani tsari don duba yanayin yadda cutar mai kisa ke ƴaɗuwa a jihar.
Ya ce abin da ya janyo ƴaɗuwar cutar shi ne wahala wajen kai wa garuruwan da ke da nisa, idan ana batun kai magunguna.
Mece ce mashaƙo
Dr Usman Bashir, likitan kula da lafiyar al’umma ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke Kano, ya ce cutar mashako dai wata cuta ce da ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60.
Dr Usman ya ce cutar tana an fi samunta a wuraren da ba a fiya yin alluran rigakafi ba. Kama garkuwar jikin ɗan adam take kamawa ta yi mata mummunar illa.
Likitan ya ce cutar tana saurin kisa saboda ba a gane ta da wuri idan an kamu, kuma a mafi yawan lokuta sai ta kai ga yaro ya fara numfashi cikin wahala, ko kumaya gaza cin abinci ko ya kamu da zazzabi mai tsanani ko kuma yawan tari.
Ya ce cutar na yaɗuwa ne ta hanyar zama cikin cunkoso a ɗaki ɗaya, musamman wanda aka rufe tagoginsa babu wajen shan iska da kuma waɗanda ba a yi wa allurar rigakafi ba wadda ke bayar da garkuwa ga kwayoyin halittar ɗan adam da ke yaƙar kwayoyin cutar.
Ya kuma ce tana ɗaya daga cikin cutukan yara da ke saurin kisa, sannan tafi tashi a lokacin sanyi.
Alamomin cutar mashaƙo
Dr Usman Bashir ya ce alamomin cutar na fara bayyana a jiki ne cikin kwanaki biyu zuwa biyar.
Ga dai wasu daga cikin alamomin cutar:
- Tari
- Zazzabi mai zafi
- Rashin cin abinci
- Kumburin cikin baki.
- Numfashi sama-sama
- Yoyon hanci
- Gajiya
Hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar mashaƙo
Likitan ya ce hanya daya ta kaucewa kamuwa da cutar mashako ga manya da kananan yara ita ce yin allura saboda za ta kashe kwayoyin cutar da ke jikin mutum.
Ya ce yana da muhimmanci a wayar da kan al’umma wajen yi wa yara alluran rigakafi domin hakan zai iya magance ba wai mashako kadai ba har da cutar sarkewar hakora da kyanda da sauransu.