Barasa ta hallaka mutum shida a Ogun

0
130

Wasu mutum shida sun gamu da ajalinsu bayan sun sha wata barasa da wani abokinsu ya kawo masu.

Ya kai musu barasar ne domin su sha su yi nishadi bayan sun warware wani rikici a tsakaninsu.

Lamarin ya faru a yankin Ogbogbo da ke arewacin lardin Ijebu a jihar Ogun. Wakilinmu ya gano cewa mutum 6 cikin abokan 7 da suka sha barasar ne suka mutu yayin da wanda ya ba su barasar wadda yazo da ita daga gidansa, bai sha ba, kuma bai mutu ba, sai dai ya tsere bayan faruwar lamarin.

Shaidu sun ce mutum biyu ne suka fara mutuwa bayan sun isa gidajensu yayin da aka garzaya da mutum hudu asibiti wadanda suma daga bisani suka mutu.

Kafin faruwar lamarin mutane shida da suka mutu tare da wanda ake zargin ya ba su barasar, gardama ta barke a tsakaninsu kafin daga bisani suka sasanta.

Bayan sasancin ne sai suka yanke shawarar su sha barasar domin suyi nishadi, inda wanda ake zargin ya tafi gidansa ya taho masu da barasar inda shi kuma ya ki sha.

Gidan talabijin na Channels a Nijeriya ya ruwaito jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Omolola Odutola inda ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Tabbas na samu labarin afkuwar lamarin, sai dai dangin mamatan sun nuna ba sa son a daga maganar inda suka fi so su mayar da hankali wurin binne ‘yan uwan nasu” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here