Chelsea da Al-Hilal na gogayya kan neman Mbappe

0
144

Chelsea da kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya sun fara zawarcin Kylian Mbappe, wanda bai bi tawagar PSG wasannin shirya wa kaka mai zuwa ba a Asia. (RMC Sport )

Al-Hilal ta yi wa Mbappe irin tayin da ta yi wa Lionel Messi na Yuro miliyan 400 a duk shekara, har zuwa shekara 2026, ko da yake akwai yarjejeniya ta baka tsakanin dan wasan na Faransa da Real Madrid, cewa zai koma can idan kwantiraginsa ya kare da PSG a bazara mai zuwa. (Nicolo Schira)

Yanzu dai Mbappe ya kwammace ya zauna haka ba tare da wasa ba, tsawon kakar nan gaba daya, domin ya bar PSG ba tare da kwantiragi a kansa ba a bazara mai zuwa, bayan da PSG ta sanya shi a kasuwa ranar Juma’a. (Sky Sports)

An ga matar Harry Kane a Munich, tana neman gida da makarantu, bisa ga dukkan alamu a shirye-shiryen da suke yi na komawar dan wasan na Tottenham Bayern Munich. (Bild)

Chelsea ta tuntubi Ajax inda ta bayyana sha’awarta ta sayen dan wasan tsakiya na Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 22. (The Athletic)

Maganar kwantiragin Victor Osimhen da Napoli har yanzu tana kasa tana dabo, wanda hakan ya bude kofa ga Chelsea ko Manchester United su sayi dan wasan na Najeriya. (Corriere dello Sport daga Goal)

Inter Milan ta yi amanna cewa a yanzu ba ta yadda za ta sake dawo da Romelu Lukaku kungiyar daga Chelsea bayan da dan wasan na Belgium ya yi magana da abokan hamayyarsu AC Milan da Juventus don komawa can. (Gazzetta dello Sport)

Galatasaray ta yi wa Wilfried Zaha, tayin albashin kusan fam miliyan 8 a shekara, bayan da kwantiraginsa ya kare da Crystal Palace. (Mail)

A shirye Luis Suarez, mai shekara 36, yake ya fitar da kudi daga aljihunsu ya biya domin ya bar kungiyar Gremio, domin ya sake haduwa da Lionel Messi a Inter Miami. (ESPN daga Sport)

An sheda wa Manchester City cewa dole ta biya RB Leipzig Fam miliyan 87 lakadan idan tana son matashin dan bayan Croatia, Josko Gvardiol, mai shekara 21. (Sunday Mirror)

Crystal Palace na tunanin sayen dan bayan Manchester City Aymeric Laporte, dan Sifaniya. (Star Sunday)

Manchester United na shirin kara rike Aaron Wan-Bissaka, tsawon shekara daya kamar yadda yarjejeniyarsa ta tanada, duk da cewa Crystal Palace na sha’awar sake daukarsa. (Sunday Sun)

Fulham na shirin kashe sama da Fam miliyan 30 don sayen sababbin ‘yan baya biyu, Mohammed Salisu, na Ghana, mai shekara 24, da ke Southampton da Calvin Bassey, mai shekara 23, dan Najeriya haihuwar Italiya, da ke Ajax. (Sunday Telegraph)

Dan wasan gaba na Jamaica Michail Antonio, na sha’awar barin West Ham domin ya tafi kungiyar Saudiyya da Steven Gerrard ke yi wa kociya, Al-Ettifaq, a bazaran nan. (Football Insider)

Dan gaban Ingila Ivan Toney, na duba yuwuwar sauya wakilansa, abin da ke nuna alamun cewa zai bar Brentford tun kafin haramcin wasan da aka yi masa na wata takwas kan saba dokokin caca, ya kare a watan Janairu. (Sun)

Manchester United na ganin Fam miliyan 50 zuwa 60, shi ne farashin da ya dace da matashin dan wasan Atalanta, Rasmus Hojlund, dan Denmark mai shekara 20. (Football Insider)

Kociyan Brighton Roberto De Zerbi ya nuna alamun yin musayar ‘yan wasa tsakaninsa da Chelsea, inda Blues din za su bayar da dan bayansu Levi Colwill, na Ingila, mai shekara 20, domin samun Moises Caicedo, dan Ecuador, mai shekara 21. (Talksport)

Har yanzu Liverpool na tuntubar Southampton a kan cinikin dan wasanta na tsakiya Romeo Lavia, na Belgium mai shekara 19, kuma tana da kwarin gwiwa cewa cinikin zai kammala zuwan karshen watan nan na Yuli. (Football Insider)

Southampton ta yi watsi da sabon tayin da Newcastle ta yi wa matashin dan bayanta na tawagar kasa da shekara 21 ta Ingila, Tino Livramento, mai shekara 20. (Talksport)

Dan wasan gaba na gefe na Watford, Ismaila Sarr, na Senegal na dab da komawa Marseille duk da sha’awarsa da Everton, ke yi, kuma hakan ba zai shafi zawarcin da kungiyar ta Faransa ke yi wa, dan gaba, Iliman Ndiaye, shi ma dan Senegal da ke kungiyar Sheffield ba. (FootMercato)

Manchester United na shirin sanar da sayen tagwayen ‘yan wasa Jack da Tyler Fletcher, ‘ya’yan tsohon dan wasan tsakiya na United din, Darren Fletcher, daga Manchester City a cinikin da ba a taba yi ba na ‘yan kasa da shekara 16 a Birtaniya. (Fabrizio Romano)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here