Elon Musk zai sauya tambarin Twitter

0
134

Shahararren mai kudin nan na duniya kuma shugaban kamfanin Twitter Elon Musk ya ce yana so shirin sauya tambarin Twitter.

Musk ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafin na Twitter da safiyar Lahadi.

“Nan ba da jimawa ba za mu yi sallama da tambarin twitter kuma a hankali da duka tsuntsayen”.

Shugaban kamfanin na Tesla ya kuma kara da cewa idan ya sauya sabon tambari a cikin daren, washe gari zai sa ya fara aiki a fadin duniya.

Musk ya wallafa wani hoto mai tambarin “X” inda daga baya a wani dandalin tattaunawa da murya na Twitter ya bayar da amsa bayan an tambaye shi kan cewa idan zai sauya tambarin inda ya ce “Eh, ya kamata a ce tun tuni an sauya shi”.

Kamfanin Twitter ya sha caccaka a ’yan kwanakin nan bayan matakin da kamfanin ya ce zai dauka na kayyade adadin sakonnin da mutum zai iya karantawa a duk rana.

Jim kadan bayan hakan sai kamfanin Meta da ke adawa da Twitter ya fitar da sabuwar manhaja mai suna Threads wadda miliyoyin mutane suka yi rajista.

Hakan ya harzuka shugaban kamfanin na Twitter inda ya sha alwashin shigar da kara a gaban kotu.

Tun can dama kamfanin na Twitter yana shan suka iri-iri kan wasu matakai da ya rinka dauka a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here