Jihar Kano ce kan gaba a yawan masu fama da cutar Mashako – NCDC

0
128

Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce cutar mashako (diphtheria) ta kashe mutum 80 a kasar daga watan Mayu zuwa Yunin bana.

A rahoton da hukumar ta fitar ta ce yanzu mutum 836 suka harbu da cutar kuma jihar Kano ce ta fi yawan wadanda suka kamu da ke da mutum 819.

Hukumar ta ce alkaluman sun shafi kananan hukumomi 33 na jihohi bakwai da suka hada da Yobe da Katsina da Sokoto Zamfara da Kaduna da kuma Abuja.

Ko a makon nan an bayar da rahoton mutuwar yara kusan 10 sakamakon cutar a jihar Kaduna

Tsohon shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriyar Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC Hausa cewa halin da aka tsinci kai a ciki abun tashin hankali ne, ba na wasa ba.

Ya ce dole ne a tashi a dauki mataki, idan kuwa ba haka ba za a ji kunya.

”Ina mamaki kwarai, tunda bai kamata a ce ana yi wa yara rigakafin wannan cuta tun farko amma kuma ana samunta ba, abun ma da muke gani da ke tabbatar mana da cewa an gaza ne wajen yin rigakafin ko kuma wasu ba sa kai ‘ya’yansu a musu rigakafin shi ne kaso 80 ba a musu rigakafin ba.”

Ya ce wannan babbar gazawa ce da ke nuna ya kamata gwamnati da hukumomi su tashi su yi wa kansu kiyamallaili.

Farfesa Abdussalam Nasidi, ya kara da cewa a halin da ake ciki, idan har mutum ya kamu da cutar to ba lallai ne rigakafin ya yi aiki a kansa ba, ballantana da a yanzu haka ana fama da karancin rigakafin shi kansa.

Yadda cutar ke kama mutum

Masanin ya bayyana wa BBC cewa cutar mashakon, na kama makogaro ne, ta hana mutum sakat.

Ya ce: ”Idan ta kama mutum za ta rike masa wuya kamar an shake ka, idan ta kama yaro idan ba Allah ne Ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babban barazana ce”

Likitoci sun ce hanya daya ta kauce wa kamuwa da cutar mashako ga manya da kananan yara ita ce yin allura saboda za ta kashe kwayoyin cutar da ke jikin mutum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here